Yan bindiga sun harbe yan sanda 2, sun yi awon gaba da 7 a Adamawa

Yan bindiga sun harbe yan sanda 2, sun yi awon gaba da 7 a Adamawa

Wasu yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun kai mumunan hari jihar Adamawa inda suka hallaka jami'an yan sanda biyu tare da awon gaba da mutane bakwai.

Shugaban karamar hukumar Mubi ta kudu, Ahmadu Dahiru, ya bayyanawa manema labarai cewa maharan sun aikata ta'asan ne a hanyan Mubi zuwa Gyela ranar Talata.

Yace: "Masu garkuwa da mutane sun addabi garuruwanmu. Kulli yaumin suna garkuwa da mutane babu dare, babu rana."

"Sun kashe yan sanda biyu dake sintiri a ranar Talatan da ya gabata a hanyar Mubi-Gyela. A yanzu haka, kwanaki uku da suka gabata an sace mutane biyar a Kwaja, sannan biyu a kauyen Sauda."

Ya ce masu garkuwa da mutanen na boyewa ne kan tsaunin dake iyakar Najeriya da Kamaru kuma iyalai da dama sun yi asarar miliyoyi sakamakon haka.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, DSP Sulaiman Nguruje, ya tabbatar da aukuwar wannan kuma ya ce tuni an tura jami'an tsaro wajen.

Ya yi kira da al'ummar jihar sun kai karan duk wani bakon abun da suka lura a unguwanninsu.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel