'Yan bindiga sun farwa jami'an FRSC bayan sun kashe 'yan kwallo

'Yan bindiga sun farwa jami'an FRSC bayan sun kashe 'yan kwallo

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, a ranar Juma’a, sun kai wa jami’an FRSC hari. Sun kasha mutum daya inda suka bar daya cikin halin mummunan rauni.

A takardar da mai magana da yawun hukumar ya fitar a ranar Asabar, Bisi Kazeem, ya ce an hari jami’ansu biyu da ke kan hanyar zuwa Legas da misalin karfe 1:50 na rana.

“Jami’anmu biyu na tafiya a mota kirar Toyota Hilux. ‘Yan bindiga sun haresu a kan titin Zairagi a titin Lokoja zuwa Okene, kusa da Lokoja, jihar Kogi,” in ji shi.

Kazeem ya ce ‘yan bindigar sun bude wa jami’anmu wuta bayan da suka hango motarsu. Sun bude musu wuta inda suka samu direban a kai kuma ya mutu a take.

DUBA WANNAN: Abinda yasa ba zamu amince da hukunci kisa ga masu satar kudin kasa ba - Majalisa Dattawa

“Tuni motar ta kubce tare da barin kan titi. An samu sa’o’i da yawa kafin a samu tseratar da motar tare da jami’an da suka yi cikin daji,” in ji shi.

Shugaban hukumar Boboye Oyeyemi, ya mika jajensa ga iyalan wadanda abun ya rutsa dasu, hukumar kiyaye hadurran kan titin da ma’aikatan hukumar da kuma kasar baki daya a kan wannan rashin da aka yi.

An hari jami’an hukumar ne bayan mintuna 20 da aka budewa motar ‘yan kwallon kafa wuta. An hari bas din da wajen karfe 1:30 na yammaci a Kabba, kusa da Lokoja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel