Tirkashi: Bidiyon yadda wani Fasto yake yiwa mambobinsa bulala saboda sun daina zuwa coci

Tirkashi: Bidiyon yadda wani Fasto yake yiwa mambobinsa bulala saboda sun daina zuwa coci

- Bidiyon wani fasto dan kasar Uganda ya jawo maganganu daban-daban ga ma’abota soshiyal midiya

- A bidiyon, an ga faston na zanar mambobin cocin a kan zarginsu da ya yi da rashin zuwa coci

- An ga mutanen sun kwanta kasa warwas inda faston ke bi sahu-sahu da bulalarshi yana tsabga

Wani sabon bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumuntar zamani ya jawo surutai daga mutane da yawa. Wani fasto dan kasar Uganda mai suna Paul Muwanguzi ne aka hango yana zane mambobin cocin, a kan zarginsu da yayi da kin zuwa coci.

A bidiyon, an ga mutanen na kwance kasa yayin da yake binsu daya bayan daya yana zane musu jiki. Bayan ya gama zanarsu, sai su koma wajen zamansu.

Tuni dai bidiyon ya jawo cece-kuce daga ma’abota amfani da kafafen sada zumuntar zamani. Wasu na son gano hikimar da ta ke kunshe a kan zanar mambobin cocin bayan duk ba yara bane.

A wani kuma lamarin da ya faru a Najeriya, wani ma’aboci amfani da kafar sada zumunta zamani ta tuwita, Kevin Odanz, ya bayyana yadda wani fasto a Kubwa, Abuja ya gina tafkin wankan zamani wanda ake kiar da ‘Swimming pool’ a cikin majami’ar, wanda ya sanya wa suna ‘pool of bethsheba’.

KU KARANTA: Shikenan: Mutumin da ya shafe shekaru 12 a gidan yari akan laifin da bai aikata ba yanzu ya zama lauya

An zargi cewa wajen wankan na da wani iko na waraka kuma mutum na shiga, dukkan matsalolinshi ke tafiya.

Amma kuma, faston na karbar N50,000 daga mabiyanshi masu bukatar waraka. Ga wadanda bazasu iya biyan N50,000 ba, ana diban musu kwalba daya daga cikin ruwan a N10,000.

Hakazalika, a wasu ranakun, a kan bar mutane su yi iyo tare da wanka a tafkin a kyauta ba tare da an karba ko sisinsu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel