Abinda yasa ba zamu amince da hukunci kisa ga masu satar kudin kasa ba - Majalisa Dattawa

Abinda yasa ba zamu amince da hukunci kisa ga masu satar kudin kasa ba - Majalisa Dattawa

Majalisar dattawa ta ce ba zai yiwu a kirkiro da dokar kisa ga mahandama ba. Amma kuma, majalisar dattawan ta ce a shirye take da ta goyi bayan wasu hukuncin da za a yi wa mahandaman.

Mai magana da yawun majalisar, Godiya Akwashiki ya sanar da hakan yayin zantawarsa da wakilin jaridar The Punch.

Ya yi magana ne a kan yadda wasu ‘yan Najeriya ke kira ga majalisar a kan ta yankewa masu wawurar kudin kasa hukuncin kisa, a maimakon masu kalaman kiyayya a kafafen sada zumuntar zamani.

Akwashiki ya kara da yin bayanin cewa, ba zai yiwu shugaban majalisar dattawan ya umarci wani sanata da ya miko wata bukata gaban majalisar ba, harda wanda ya hada da kisa ga mahandama.

“Ba zai yiwu shugaban majalisar dattawan ya umarci wani sanata da ya miko wata bukata gaban majalisar ba . Dukkanmu muna wakiltar mazabunmu ne daga sassa daban daban na kasar nan,” in ji shi.

DUBA WANNAN: Ra'ayin Aisha Buhari da na Sarkin Musulmi sun banbanta kan dokar soshiyal midiya

Mai magana da yawun majalisar ya bayyana cewa, akwai hukunce-hukunce da aka tanadar ga shuwagabanni mahandama da masu wawurar dukiyar kasa. Wannan hukunce-hukuncen kuwa suna nan tattare a cikin dokokin ICPC da EFCC.

“Muna da dokokin ICPC da EFCC da aka shinfida don masu wawurar kudin kasa. Ina so in tabbatar muku da cewa, muna tafiya a hankali ne. Duk wani hukuncin da za a kawo gaban majalisar, muna maraba da shi,” in ji shi.

Akwashiki, ya kara da yin kira ga bangarorin gwamnati, kungiyoyi da sauran jama’a da su miko bukatar kisan ga mahandaman har zuwa majalisar dattawan.

Ya musanta zargin da ake ga sanataocin na cewa da ake ba za su aminta dashi ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel