2023: Akwai yiwuwar dan arewa ne zai karba mulki daga hannun Buhari, inji Babatope

2023: Akwai yiwuwar dan arewa ne zai karba mulki daga hannun Buhari, inji Babatope

- Tsohon ministan sufuri, Cif Ebenezer Babatope ya bayyana ra'ayinsa kan kan zaben shugaban kasa na 2023

- Jigon na jam'iyyar PDP kuma mamba a kwamitin amintattu na jam'iyyar yana ganin akwai yiwuwar wani dan arewa ne zai maye gurbin Shugaba Buhari

- Babatope ya yi hasashensa ne duba da cewa babu tsarin karba-karba ba a kudin tsarin mulkin jam'iyyar APC

Tsohon ministan sufurin Najeriya, Cif Ebenezer Babatope ya yi hasashen cewa wani dan arewa ne zai zama shugaban kasa bayan wa'adin Shugaba Muhammadu Buhari ta za karshe a 2023.

Babatope wanda mamba ne na kwamitin amintattu na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya bayyana hakan ne yayin wata zantawa da ya yi da jaridar Daily Sun.

Tsohon ministan ya yi nuni da cewa babu tsarin karba-karba ba a kudin tsarin kundin tsarin mulkin jam'iyyar APC ta zai tilastawa jam'iyyar bawa wani yankin takara.

Ya ce 'yan jam'iyyar APC daga kudancin Najeriya da ke neman a bawa yankinsu damar tsayar da dan takarar shugaban kasa suna bata lokacinsu ne kawai.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Kotu ta tuɓe rawanin wani babban sarki mai daraja ta ɗaya a Najeriya

Kalamansa: "'Yan jam'iyyar APC daga kudancin Najeriya da ke cewa kada a soke tsarin karba-karba tare da cewa lokaci ya yi da za a bawa kudu damar fitar da dan takarar shugaban kasa ba su san cewa babu tsarin karba-karba a kundin tsarin jam'iyyar APC."

"El-Rufai da sauran wadanda ke da ra'ayi irin nasa daga Arewa za suyi amfani da wannan damar, kuma hakan zai ya haifar da yanayi da jam'iyyar za ta sake tsayar da dan arewa a 2023.

"Saboda haka 'yan jam'iyyar APC daga yankin kudu da ke neman yankinsu ta fitar da shugabancin kasa akwai yiwuwar mafarki kawai su keyi."

Da ya ke magana kan yankin da ya dace ta fitar da shugaban kasa, Babatope ya ce Kudu maso gabas ya dace ta fitar sa shugaban kasar.

Ya ce, "Ina ganin ya dace mu bawa Kudu maso gabas damar fitar da shugaban kasa na gaba. Ina ganin ya dace Igbo su samu a 2023.

"Idan dai muna mulki na tarayya ne, ya kamata Kudu maso gabas su samu a 2023. Amma wannan ra'ayi na ne kawai.

"Jam'iyya ce za ta zartar da hukunci, kuma a matsayi na na dan jam'iyya mai biyaya, zan goyi bayan duk abinda ta tsayar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel