Zaben Kogi: Bayan neman a dage zabe, Dino Melaye ya jefa kuri'arsa

Zaben Kogi: Bayan neman a dage zabe, Dino Melaye ya jefa kuri'arsa

Duk da nema da ya yi a dage zabe, dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) Sanata Dino Melaye ya tafi wurin zabe ya kada kuri'asa a zaben raba gardama da ake maimaitawa a jihar Kogi.

Melaye ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Asabar 30 ga watan Nuwamba cewa ya kama jefa kuri'asa.

Idan ba a manta ba an soke zaben na ranar 16 ga watan Nuwamba ne sakamakon rikice-rikice, satar akwatin zabe da barazana da aka rika yi wa masu jefa kuri'a yayin zaben.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Kotu ta tuɓe rawanin wani babban sarki mai daraja ta ɗaya a Najeriya

Sai dai duk da haka, Melaye bai so a gudanar da karashen zaben ba inda ya shigar da Hukumar zabe mai zaman kanta INEC kara a kotu yana neman kada ayi zaben.

Melaye ya kuma sake bibiyar INEC a ranar Labara 27 ga watan Nuwamba da wata karar inda ya ke bukata hukumar ta dauki mataki kan karar da ya shigar na neman kada a gudanar da zaben na karashe.

Dan takarar na PDP ya bukaci INEC ta dage zaben a kan dalilinsa na cewa hukumar zaben ta cire wasu mazabu da aka soke zabensu na ranar 16 ga watan Nuwamba a zaben na karashe da za a gudanar.

An ruwaito cewa kwamishinan INEC na kasa baya ofishinsa lokacin da Melaye ya tafi shigar da kararsa amma wani babban jami'in hukumar Jafaru Leko ya karbi koken na Melaye.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel