Matafiya Legas zuwa Ibadan za su shiga jirgin kasa kyauta har zuwa Maris na 2020 - FG

Matafiya Legas zuwa Ibadan za su shiga jirgin kasa kyauta har zuwa Maris na 2020 - FG

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa za a dauki matafiya kyauta a jirgin kasa daga Lagos zuwa Ibadan.

Ministan sufuri na kasa, Mista Chibuike Amaechi ne ya bayar da sanarwar a ranar Asabar 30 ga watan Nuwamba a shafinsa na Twitter.

Ya yi bayyanin cewa jirgin zai tashi ne daga tashar jirgi na Iju a Legas kuma za a cigaba da daukan mutane kyauta har bayan bukukuwan Kirsimeti da sabon shekara.

Ameachi ya ce za a cigaba da jigilar fasinjoji kyauta har zuwa watan Maris na 2020.

Ya shawarci matafiya kada su bari a bar su a baya wurin morar lagwadan na 'tafiya zuwa next level'

Ga dai abinda ministan ya wallafa a shafinsa na Twitter.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Kotu ta tuɓe rawanin wani babban sarki mai daraja ta ɗaya a Najeriya

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel