Ra'ayin Aisha Buhari da na Sarkin Musulmi sun banbanta kan dokar soshiyal midiya

Ra'ayin Aisha Buhari da na Sarkin Musulmi sun banbanta kan dokar soshiyal midiya

Uwargidan shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari ta yi kira a kan dokar kafafen sada zumuntar zamani. Ta bayar da misali da kasar China masu mutane biliyan 1.3 sun yi hakan.

Ta kara da kalubalantar gwamnonin jiha ta yadda suka kasa samar da ababen more rayuwa ga jama’ar jihohin.

Ta ce abubuwa sun yi wa mai gidanta yawa, shi kadai ba zai iya kawar da kalubalen da kasar nan ke fuskanta ba. Ta yi kira ga shuwagabanni da su hada kai wajen shawo kan matsalolin kasar nan.

Ta bayyana hakan ne a taron majalisar koli ta kula da al’amuran addinin musulunci da aka yi a masallacin kasa da ke Abuja.

Ya ce, ”a kan dokar kafafen sada zumunta, ba zai yuwu mutum ya karkace daga gidansa ya wallafa cewa mataimakin shugaban kasa ya yi murabus ba. Wannan babbar magana ce. Idan kasar China da ke da mutane 1.3 billion zasu iya kwaba wa mutanensu, ban ga dalili da zai sa Najeriya mai mutane miliyan 180 za su kasa kwaba wa nasu ba.”

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Kotu ta tuɓe rawanin wani babban sarki mai daraja ta ɗaya a Najeriya

A yayin bude taron da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo yayi, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su kasance masu kaunar juna duk da banbancin addinai.

Ya ce, “A tunani na, yadda za a gyara kasar nan ya ta’allaka ne ga shuwagabanninmu. Mu kasance masu kaunar juna duk da banbancin addinai. Muna da matsalolin kabilanci da na addini da suka mana yawa. Mutane da yawa na buga gangar yakin kabila da na addinai.”

A jawabin mai girma sarkin musulmai, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III a yayin bude taron, ya yi kira ga jama’ar kasar nan da su hada kansu. Ya jaddada cewa, matsalar karatun yara mata da kuma almajiranci, dole ne a shawo kanta da wuri.

“Na samu kiraye-kiraye a kan maganar dokar kafafen sada zumunta. Wasu mutanen cewa suke yi a yi dokar kalaman kiyayya. Dole ne mu karbi hukuncin da mutane suka yanke. Duk da cewa, su ne suka zabi shuwagabannin. Ya kamata mu sauraresu, akwai bukatar mu bi ra’ayinsu,” in ji Sultan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel