An yanke wa shugaban kasar Suriname hukuncin shekaru 20 a gidan yari kan kashe-kashen 1982

An yanke wa shugaban kasar Suriname hukuncin shekaru 20 a gidan yari kan kashe-kashen 1982

Wata kotun sojoji a kasar Suriname ta yanke wa Shugaba Desi Bouterse hukuncin zaman gidan yari na shekaru 20 a ranar Juma'a saboda kashe-kashen abokan hamyyarsa da ya yi lokacin yana shugabancin kasar da ke nahiyar Kudancin Amurka a 1980s.

Bouterse mai shekaru 74 da haihuwa ya kai wata ziyarar aiki kasar China kuma zai daukaka karar idan ya dawo a mako mai zuwa a cewar lauyansa Irvin Kanhai kamar yadda Channels Television ta ruwaito.

Bouterse ya mamaye siyasar kasar ta Bouterse tun bayan lokacin da ya hau kan mulki a 1980.

Wasu alkalai uku ne suka zartar da hukuncin na ranar Juma'a karkashin jagorancin mai shari'a Cynthia Valstein-Montor kan wasu kashe-kashen gilla 15 da ya yi wa masu adawa da gwamnatinsa a 1982.

Kashe-kashen na Disamba inda gwamnatinsa ta kama farar hula 13 da sojoji biyu ta kashe su ba tare da hakki ba ya kasance daya daga cikin abubuwan da ya janyo wa Bouterse bakin jini.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Kotu ta tuɓe rawanin wani babban sarki mai daraja ta ɗaya a Najeriya

Bouterse ya dade yana musanta cewa yana da hannu cikin kisar inda ya ce an kama mutanen ne kan laifin shirya juyin mulki tare da taimakon hukumar leken asiri na Amurka CIA kuma an harbe su ne yayin da suke kokarin tserewa.

Hujojjin da ya bayar sun ci karo da wanda shaidun da ke wurin lokacin da abin ya faru suka bayar inda suka ce yana wurin lokacin da aka harbe mutanen a Fort Zeelandia a babban birnin kasar Parammaribo.

A hukuncin ta, Valstein ta ce Bouterse ya taka muhimmiyar rawa wurin kisar duk da cewa yana da ikon ya hana a kashe su.

Lauyoyin sojoji ne suka sake waiwayar shari'ar a Bourtese da wasu mutum 24 da ak zargi a 2007 amma shugaban kasar da wasu 'yan siyasa masu masa biyaya sun ta kokarin kawo cikas ga shari'ar.

Shari'ar ta yi tsawo sosai inda aka kwashe shekaru 12 ana yi tuni ma har mutum shida cikin wadanda ake zargi sun mutu.

A karkashin dokar Surinamese ba za a iya kama shugaban kasar ba har sai dukkan damar da ya ke da shi na daukaka karar sun kare hakan na nuna cewa akwai yiwuwar ba zai tafi gidan yari ba a yanzu.

Kasar ta Suriname ta samu 'yanci ne daga hannun Netherlands a 1975.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel