Innalillahi: Wani mutumi ya yiwa daliba fyade sannan ya kasheta ta hanyar caka mata wuka sau 52

Innalillahi: Wani mutumi ya yiwa daliba fyade sannan ya kasheta ta hanyar caka mata wuka sau 52

- Hukumar ‘yan sandan kasar Afirka ta Kudu sun cafke wani mutum da ake zargi da fyade da kisan kai

- Ya shiga dakin dalibar budurwar ne ta taga inda ya afka mata tare da sukarta da wuka har sau 53

- Bayan kururuwarta da ihu ne makwabtanta suka kira jami’an ‘yan sanda wadanda suka tarar da ita a cikin jini

Hukumar ‘yan sandan kasar Afirka ta Kudu ta cafke wani mutum da ake zargi da fyade tare da kisan gilla ga wata budurwa mai shekaru 21 a duniya.

An zargi mutumin da sukar budurwar mai suna Precious Ramabulana bayan fyaden da yayi mata. Lamarin ya faru ne a kwalejin Capricon TVET, Limpopo a kasar Afirka ta Kudu inda take karatu a fannin kasuwanci.

Kamar yadda rahoto ya nuna, an gano cewa saurayin ya soke ta da wuka har sau 53 a wurare daban-daban na jikinta a ranar Lahadi da misalin karfe 2 na dare.

Kakakin hukumar ‘yan sandan yakin, Brig Motlafela Mojapelo ne ya sanar da hakan. Ya bayyana yadda dalibar take kwance a gidan da take haya cikin dakinta amma mutumin da ba a sani ba ya kai mata mummunan hari.

KU KARANTA: Shehu Sani: Abin da yasa muka ki yarda Buhari ya ciyo bashin $30bn a lokacin Saraki

“An zargi cewa, wacce ta rasun na kwance ne a dakinta da ke sashin GaJoel na Mokomene, inda wanda ake zargin ya samu shiga. Ya shiga dakin nata ne ta taga kuma ya kai mata farmaki. Ya soke ta sau da yawa kuma ya tsere. Makwabtanta sun ji ihunta da kururuwarta wanda hakan ya yi sanadin da suka kira ‘yan sanda.”

“Bayan isowar ‘yan sandan, an samu gangar jikinta kwance cikin jini tsundum da kuma shaidar sukar ta da aka yi da wuka. Har yanzu dai ba a san dalilin kai harin ba,” Mojapelo ya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel