Shehu Sani: Abin da yasa muka ki yarda Buhari ya ciyo bashin $30bn a lokacin Saraki

Shehu Sani: Abin da yasa muka ki yarda Buhari ya ciyo bashin $30bn a lokacin Saraki

- Tsohon dan majalisar tarayya, Shehu Sani, ya yi karin haske a kan dalilin da yasa suka yi watsi da bukatar aron kudi a majalisa kashi ta 8

- Sani ya bayyana cewa, wannan bashin zai kawo zagon kas ga kasar nan ta yadda zamu zama bayi kuma tamkar ‘yan haya a kasarmu

- Majalisar tarayyar a wancan lokacin ta ki amincewa da bukatar, amma sai gashi shugaba Buhari ya garzayo da ita gaban sabuwar majalisa

Tsohon dan majalisa, Shehu Sani, wanda ya yi shugabancin kwamitin bashin cikin gida da waje a majalisar tarayya karo na 8, ya yi bayanin abinda ya sa suka soki karbo bashin shugaban kasa Muhammadu Buhari har na $29.96 billion a majalisar karo ta takwas.

Kamar yadda wata takarda da Shehu Sani ya fitar a ranar Juma’a ta sanar, “majalisar ta yi watsi da bukatar ne don gujewa ‘yan Najeriya ‘mulkin mallakar bankunan bashi”.

A shekarar 2016 ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya garzaya majalisar dattawan da bukatar ta amince da tsarin bashin 2016 zuwa 2018 na gwamnatin tarayya.

Tuni dai majalisar karo ta takwas ta ki amincewa da wannan bukata. Amma a halin yanzu, shugaban kasar ya garzaya gaban majalisar dattawan kashi ta tara da wannan bukatar. Ya bayyana cewa, akwai matukar amfani idan suka amince da tsarin bashin, wanda ya ce, “zai taka rawar gani a bangaren tsare-tsare da shirye-shirye na gwamnatin”.

Amma kuma, a mayar da martanin da Sani ya yi, yace bashin kasar nan zai kai $52 billion idan da an aro kudin a wancan lokacin.

KU KARANTA: Tafkin waraka: Wani fasto ya gina tafki dake warkar da dukkan cuta, yana karbar N50,000 kafin a yi wanka a ciki

“Mun ki amincewa da karbo bashin ne saboda mu tseratar da ‘yan Najeriya daga fadawa mummunan tarkon masu bada bashin. Ba mu da bukatar bankunan masu bada bashin su koma mana mulkin mallaka.” in ji shi.

“Idan bashin da ake binmu ya yi tashin gwauron zabi, akwai yuwuwar mu fada matsalar bauta sannan mu koma ‘yan haya a kasarmu ta gado. Zasu ce maka, ko Amurka na rance amma bansan dalilin da zai sa mu cigaba da ranto kudi ba don wasu kasashen na yi.”

“Idan muka cigaba da jin shawarwarin ma’aikatan bankuna da ‘yan kwangila kuma muka cigaba da binne kanmu, akwai yiwuwar mu bar ‘ya’yanmu da wani nauyi a kai. Bashi ba sadaka bane. Da yawa daga cikin masu zuga mu karbar bashi su ke amfana. Dole ne mu kiyaye.” In ji Sani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel