Tafkin waraka: Wani fasto ya gina tafki dake warkar da dukkan cuta, yana karbar N50,000 kafin a yi wanka a ciki

Tafkin waraka: Wani fasto ya gina tafki dake warkar da dukkan cuta, yana karbar N50,000 kafin a yi wanka a ciki

- Wani ma’aboci amfani da tuwita ya wallafa yadda wani fasto ya gina tafkin waraka a Kubwa, Abuja

- Tafkin dai na cike da abun mamaki, domin kuwa ana shiga aka yi wanka matsalolin mutum ke gushewa

- Amma kafin a shiga sai an biya N50,000, marasa karfi na siyan kwalbar ruwan tafkin a N10,000

Wani ma’aboci amfani da kafar sada zumunta zamani ta tuwita, Kevin Odanz, ya bayyana yadda wani fasto a Kubwa, Abuja ya gina tafkin wankan zamani wanda ake kiar da ‘Swimming pool’ a cikin majami’ar, wanda ya sanya wa suna ‘pool of bethsheba’.

An zargi cewa wajen wankan na da wani iko na waraka kuma mutum na shiga, dukkan matsalolinshi ke tafiya.

Amma kuma, faston na karbar N50,000 daga mabiyanshi masu bukatar waraka. Ga wadanda bazasu iya biyan N50,000 ba, ana diban musu kwalba daya daga cikin ruwan a N10,000.

Hakazalika, a wasu ranakun, a kan bar mutane su yi iyo tare da wanka a tafkin a kyauta ba tare da an karba ko sisinsu ba.

KU KARANTA: Hanyoyi biyar da matan da mazajen su suke cin zarafin su zasu bi domin kare kansu

Kevin Odanz ya bayyana yadda faston ya zama abun zargi sakamakon wasu munanan halayenshi. An zargi faston da sakin matarshi don auren wata budurwarshi da ya dirkawa ciki ‘yar asalin kasar Afirka ta Kudu. Ya tafka wannan ta’asar ta yi wa budurwar tashi ciki ne bayan da yake da aure.

Ga abinda Odanz ya wallafa: “Akwai wata majami’a a Abuja mai cike da abun mamaki. Faston ya hada wani tafkin wanka ne da ake zargin na da ‘karfin waraka’. Ana kiranshi da ‘pool of bethsheba’. A cewarshi, tafkin na iya warkar wa da mutum duk matsalolinshi. Idan kana da bukatar shiga, sai ka biya N50,000.”

“Ga marasa karfin biya kuwa, ana diban kwalba daya a N10,000 kacal. Akwai ranakun da yake bari a shiga tafkin a kyauta ba tare da an biya ba.” Cewar Odanz.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel