Gwamnonin jam’iyyar APC sun juya ma Oshiomole baya – shugaban APC a Edo

Gwamnonin jam’iyyar APC sun juya ma Oshiomole baya – shugaban APC a Edo

A yanzu haka gwamnonin jam’iyyar APC basa tare da shugaban jam’iyyarsu, Kwamared Adams Aliu Oshiomole, kamar yadda shugaban jam’iyyar APC reshen jahar Edo, Anselm Ojezua ya bayyana.

Jaridar Premium Times ta ruwaito Anslem ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da jaridar Daily Independent a ranar Juma’a, inda yace: “Gwmanonin basa tare da shi, amma basu so a ga kamar suke jagorantar yunkurin tsige shi. Abinda sukeso kawai shine ya yi amfani da hankalinsa, idan ya gane sai ya yi murabus kawai domin kuwa ban jin zai tsallake wannan tarkon.”

KU KARANTA: Labari mai dadi: Buhari zai gina sabuwar jami’ar rundunar Sojan sama a Bauchi

Shugaba Anselm ya yi wannan bayani ne bayan kammala taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC daya gudana a sakatariyar jam’iyyar dake babban birnin tarayya Abuja, inda ya zargi da shirya zagon kasa a yayin taron domin bai bari taron ya gudana kamar yadda ya kamata ba.

Shi dai Mista Anselm na hannun daman gwamnan jahar Edo, Godwin Obaseki ne, wanda kuma zaman da ake a yanzun nan suna takun saka da shugaban APC Oshiomole, a sanadiyyar haka aka samu tawariyyaha a cikin gidan jam’iyyar APC ta jahar Edo.

A kwanakin bayan ne bangaren APC gidan gwamnati suka sanar da sallamar Oshiomole daga jam’iyyar, yayin da su kuma bangaren Oshiomole suka tsige Anselm daga shugabancin jam’iyyar, sai dai wata babbar kotu dake zamant a Bini ta soke wannan tsigewa.

Haka zalika shi ma gwamnan jahar ya kakkabe duk wasu manyan jami’an gwamnatinsa daya san suna biyayya ga shugaban APC tasa kasa Adams Oshiomole ta hanyar rabasu da mukamansu.

Wannan rikici ta kai ga a yanzu haka akwai wasu yayan majalisar dokokin jahar Edo su 10 dake biyayya ga Oshiomole wanda har yanzu ba’a rantsar dasu a matsayin yan majalisu ba a dalilin wannan rikici, kuma sun tsere zuwa Abuja domin neman mafaka don gudun kada yan baranda su kai musu hari.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel