Ekiti: Shugabannin kananan hukumomi 7 na PDP sun koma APC ana saura kwanaki kalilan zabe

Ekiti: Shugabannin kananan hukumomi 7 na PDP sun koma APC ana saura kwanaki kalilan zabe

Sansanin jam'iyyar PDP na jihar Ekiti ta girgiza ana sauran kwanaki 10 zaben shuwagabannin kananan hukumomi a jihar.

Wannan girgizar ta biyo bayan canza sheka da shuwagabannin kananan hukumomi bakwai suka yi zuwa jam'iyyar APC a ranar Juma'a.

Mataimakan shuwagabannin kananan hukumomin bakwai tare da kansilolin duk sun canza shekar kamar yadda suka ga shuwagabanninsu sunyi.

Tuni dai shugaban jam'iyyar APC na jihar, Paul Omotosho da kuma gwamna jihar, Kayode Fayemi suka karbesu hannu bibbiyu.

Shugaban jam'iyyar APC na jihar ya kwatanta wannan cigaban da mummunar barna ga PDP kuma karin karfi ga APC.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Kotu ta tuɓe rawanin wani babban sarki mai daraja ta ɗaya a Najeriya

Ya ce, "Ku bar masu tunani daga cikin mambobin jam'iyyar adawa su matso kusa yanzu. A yau muna tare da ruhin jam'iyyar PDP a tare damu."

Omotosho ya kara da cewa, a yanzu APC za ta yi ajiyar zuciya kuma hankalinta zai kwanta, tunda a halin yanzu manyan kalubalen da take hangowa sun dawo bangarenta.

Gwamna Fayemi, a bangarensa, wanda ya samu wakilcin shugaban ma'aikata, Biodun Omoleye, ya tabbatar wa da masu canza shekar sun yi babban tunani.

"Muna tabbatar muku da cewa, canza shekar da kuka yi ba zaku yi dana sani ba. Muna kara tabbatar muku da cewa, matukar kune taurarin jam'iyyarku, toh kuwa a nan zaku samu wannan matsayin," in ji Gwamnan.

Masu canza shekar sun tabbatar da hukuncin da suka yanke tare da jaddada cewa, nauyin da suke tare dashi ya isa ya kara wa APC karfi tare da nasarar a zaben ranar 7 ga watan Disamba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel