Miyagu sanye da khakin NYSC sun yi harbin mai kan uwa da wabi a kan yan kwallon Najeriya

Miyagu sanye da khakin NYSC sun yi harbin mai kan uwa da wabi a kan yan kwallon Najeriya

Wasu gungun yan bindiga sanye da khakin NYSC sun bude ma wasu yan kwallon Najeriya wuta na kungiyar kwallon kafa ta Ifeanyi Ubah FC a garin Okene na jahar Kogi, inji rahoton jaridar The Cables.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Juma’a, 29 ga watan Nuwamba a yayin da yan kwallon suke kan hanyarsu ta zuwa jahar Kano inda zasu kara da kungiyar kwallon kafa ta Jigawa Golden Starts a gasar zakarun Najeriya, a ranar Lahadi.

KU KARANTA: Sojojin saman Najeriya sun zazzaga ma yan ta’adda ruwan wuta a jahar Borno

Shugaban kungiyar, Mista Chukwuma Ubah ya bayyana yadda lamarin ya faru kamar haka: “A daidai garin Okene yan bindiga suka bude mana wuta, da misalin karef 1:30 na ranar Juma’a, 29 ga watan Nuwamba.

“Yan bindigan suna sanye ne da khakin yan bautan kasa NYSC, harbin ya samu direbanmu a wani dan wasa guda daya, kuma mun wuce dasu asibiti inda suke samun kulawa, amma babu wanda ya rasa ransa.

“Muna amfani da wannan dama wajen kira ga gwamnatin tarayya, hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF, hukumar dake kula da gasar firimiya ta Najeriya, LMC dasu kara kaimi wajen samar da tsaro tare da tabbatar da shi domin kungiyoyn kwallon kasa su samu daman tafiye tafiyensu cikin aminci.” Inji shi.

Daga karshe Mista Ubah ya nemi magoya bayansu da duk masoya kwallon kafa a Najeriya su sanya su cikin addu’a duba da mawuyacin halin da suka tsinci kansu a ciki.

A wani labarin kuma, dakarun yaki da ta’addanci na rundunar Operation Lafiya Dole da Sojojin kasar Chadi sun yi ma mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram jini da majina a wani samame da suka kaddamar a kansy a ranar Alhamis, 28 ga watan Nuwamba.

Sojojin sun yi artabu da yan ta’addan ne a tsibirin Duguri dake karshen yankin Arewacin jahar Borno tare da taimakon dakarun rundunar Sojan saman Najeriya, inda suka yi ma yan ta’addan kaca kaca duk kuwa da cewa akwai yanayin danshi a yankin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel