Gwamnan Borno ya ginawa marayu 540 makaranta (Hotuna)

Gwamnan Borno ya ginawa marayu 540 makaranta (Hotuna)

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya kaddamar da makarantar da aka ginawa yara marayu akalla guda 540 a jihar.

Wani attajiri mazaunin Maiduguri ne ya daukin nauyin wannan gini gaba dayanta.

A bangarensa, gwamnan ya bada kyautan motocin da za'a rika amfani da su wajen kai yaran makaranta.

Legit.ng ta samu labarin ne a jawabin da hadimin gwamnan ya saki a shafinsa na Facebook inda yace:

"Gwamna Babagana Umara Zulum ya kaddamar da makaranta mai iya daukan marayu 540 da wani mutumin kirki ya gina."

Wani attajirin Maiduguri, Barista Zanna Mustapha, wanda yake shugaban makarantar marayu, Future Prowess, ne ya dauki nauyin ginin makarantar."

"Yaran da suka rasa iyayensu sakamakon yakin Boko Haram ne za'a baiwa ilimi kyauta.

"Gwamna Zulum ya jinjinawa Mustapha bisa taimakonsa kuma ya tabbatar masa da cewa gwamnatin jihar zata bada gudunmuwa wajen inganta koyar da su."

"Shugabar daliban wacce tayi jawabi a madadin daliban ta mika godiyarta ga gwamnan kan bada kyautan motoci domin saukaka sufurinsu zuwa makaranta."

KARANTA: Shugaba Buhari ya dira Daura domin kaddamar da sabuwar jami'ar Sufuri

Gwamnan Borno ya ginawa marayu 540 makaranta (Hotuna)

Gwamnan Borno ya ginawa marayu 540 makaranta (Hotuna)
Source: Facebook

Source: Twitter

Gwamnan Borno ya ginawa marayu 540 makaranta (Hotuna)

Gwamnan Borno ya ginawa marayu 540 makaranta (Hotuna)
Source: Facebook

Source: Legit

Tags:
Online view pixel