Sojojin saman Najeriya sun zazzaga ma yan ta’adda ruwan wuta a jahar Borno

Sojojin saman Najeriya sun zazzaga ma yan ta’adda ruwan wuta a jahar Borno

Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da cewa jiragen yakinta dake aikin tabbatar da tsaro a yankin jahar Borno a karkashin aikin Operation Lafiya Dole sun tarwatsa wasu manyan motocin yakin yan ta’addan Boko Haram guda biyu, tare da kashe mayakan dake ciki.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito rundunar ta samu wannan nasara ne a kauyen Borgozo dake jahar Borno, inda ta hangi yan Boko Haram suna tafiya a cikin motoci guda biyu, nan da nan ta tura jiragen yakinta ya sauke musu ruwan bala’i, kowa ya mutu a ciki.

KU KARANTA: Mai alfarma Sarkin Musulmi ya bayyana yau a matsayin 1 ga watan Rabiul -Thani

Kaakakin rundunar, Ibikunle Daramola ne ya tabbatar da haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Juma’a, 29 ga watan Nuwamba a babban birnin tarayya Abuja, inda yace wannan nasara ta samu ne a daidai lokacin da jiragen ke baiwa Sojojin kasa tsaro ta sama a yayin da suke artabu da yan ta’adda a yankin.

“A yayin da jiragen yakin suka isa inda yan ta’addan suke, sun hangi wasu motocin yan ta’addan suna kokarin tserewa, amma ganin jiragen sai suka boye motocin a karkashin wasu bishiyoyi, sa’annan wasu daga cikinsu suka sauka da nufin tserewa cikin daji a kasa.

“Nan da nan ba tare da bata lokaci ba jiragen suka bude musu wuta, a dalilin haka suka lalata motoci biyu daga ciki, tare da halaka mayakan dake cikinsu da wadanda suka yi kokarin tserewa.” Inji shi.

Daga karshe, Daramola yace rundunar Sojan sama za ta cigaba da aiki tare da Sojojin kasa da saukan hukumomin tsaro don tabbatar na cimma manufar karar da sauran yan Boko Haram da suka rage a yankin Arewa maso gabas.

A wani labarin kuma, Dakarun yaki da ta’addanci na rundunar Operation Lafiya Dole da Sojojin kasar Chadi sun yi ma mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram jini da majina a wani samame da suka kaddamar a kansy a ranar Alhamis, 28 ga watan Nuwamba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel