Yadda wani ministan Buhari ya hada kai da PDP a zaben wata jiha - Ubani

Yadda wani ministan Buhari ya hada kai da PDP a zaben wata jiha - Ubani

Wani jigo a jam’iyyar APC kuma tsohon dan takarar gwamnan jihar Abia karkashin jam’iyyar AAC a 2019, Ambasada Vincent Ubani, ya caccaki karamin ministan ma’adanai da karafuna, Dr Uchecukwu Ogah a kan rawar da ya taka yayin zaben jihar na 2019.

Ubani ya yi ikirarin cewa, jam’iyyar PDP ta dau nauyin karamin ministan a jihar yayin zaben ranar 23 ga watan Maris, lamarin da ya kawo koma baya ga jam’iyyar APC a jihar Abia.

Jigon APC din ya jaddada cewa, Ogah bashi da kwazon shugabancin da zai yi amfani dashi wajen juya akalar shugabanci a jihar Abia da kasar baki daya.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Kotu ta tabbatarwa gwamnan Bauchi kujerarsa, ta yi fatali da karar jam'iyyar APC

Ubani wanda ya zanta da manema labarai a garin Umuahia, babban birnin jihar a ranar Alhamis, ya zargi tsohon dan takarar gwamnan karkashin jam’iyyar APC din da kawo tawaya ga farin jinin siyasar Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma APC a yankin kudu maso gabas din.

Jigon jam’iyyar APC din ya kara da caccakar ministan a kan sabuwar biyayyar da ya fara yi wa gwamnatin Okezie-Ikpeazu bayan nada shi da aka yi cikin ‘yan majalisar zartarwar tarayya.

A yayin da manema labarai suka tambayeshi me zai ce a kan yaki da rashawa da gwamnatin Buhari ke yi, sai yace “Shugaban kasa na yaki da rashawa amma mutanen da ke kewaye dashi basa yaki da rashawar. Suna aiki ne don samar wa da cikin ‘’Kayan more rayuwa”.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel