Gwamnonin APC sun alanta Ganduje matsayin gwamna mafi aiki, ga jerin jihohin dake biye da Kano

Gwamnonin APC sun alanta Ganduje matsayin gwamna mafi aiki, ga jerin jihohin dake biye da Kano

Kungiyar gwamnonin jam'iyyar APC ta zabi gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a matsayin gwamna mafi aikin cigaban al'umma a Najeriya.

Wannan na kunshe cikin jawabin da mai magana da yawun gwamnan, Alhaji Abba Anwar, ya saki.

Jawabin ya ruwaito Dirakta Janar na kungiyar, Salihu Mohammed Lukaman, da cewa Ganduje ya samu maki 19 kuma ya zarcewa sauran gwamnonin kungiyar.

Ya jaddada cewa: "An samu kari wajen shirye-shirye da ayyukan da jihohin APC ke yi kuma jihar Kano ce ta fi yawan wadannan shirye-shirye da maki 19."

Ya bayyana cewa ana gudanar da wannan hisabi ne kan gwamnonin jam'iyyar All Progressive Congress, APC a jihohinsu kan shirye-shiryen walwala da jin dadin al'umma.

Wannan ya hada da samar da aikin yi, inganta kiwon lafiya, karfafa tsaro, sawwaka sufuri, inganta wutan lantarki, gyaran yanayi, habaka wanni da sauransu.

Ga jerin jihohin da makin da suka samu:

Kano - 19

Legas - 18

Ekiti - 17

Edo - 13

Katsina - 11

Kwara -11

Yobe - 10

Jigawa - 9

DUBA NAN: Ba zamu daga zaben gobe ba - INEC ta mayarwa Dino Melaye martani

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel