APC za ta dauki mataki kan masu neman Buhari ya zarce karo na 3, ta ce jam'iyyar adawa ce ta dauki nauyin su

APC za ta dauki mataki kan masu neman Buhari ya zarce karo na 3, ta ce jam'iyyar adawa ce ta dauki nauyin su

- A ranar Alhamis ne jam'iyyar APC ta jaddada cewa babu hannunta a maganar tazarcen shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Jam'iyyar ta ce wannan jita-jitan duk aikin 'yan adawa ne da makiya jam'iyyar don bata mata suna

- Jam'iyyar ta yi barazanar fatattakar Charles Enya, mamban da ya garzaya kotun da bukatar gyaran kundin tsarin mulki

A ranar Alhamis ne jam’iyyar APC ta jaddada cewa babu wata maganar tazarce ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Jam’iyyar ta kara da tsame kanta daga karar da Charles Enya, daya daga cikin ‘yan jam’iyyar a jihar Ebonyi, ya kai kotu don neman zarcewar shugaban kasa da gwamnoni a karo na uku.

Jam’iyyar ta ce, ‘yan adawa ne suka dau nauyin wannan al’amarin, da niyyar gwada matsayar gwamnatin shugaban Buhari a kan musanta zargin zarcewarsa a karo na uku. Jam’iyyar ta yi barazanar korar Enya da sauran masu irin halinsa, masu kawo kalubale ga damokaradiyya.

DUBA WANNAN: 'Yan siyasa 3 da PDP za ta iya tsayarwa takara idan tana son karbe mulki a 2023

“Jam’iyyar APC ta karanta a kafafen yada labarai, yadda wani dan jam’iyyar ya garzaya kotu don neman a gyara kundin tsarin mulkin kasar nan. Yana bukatar a yarjewa shugaban kasa Muhammadu Buhari tsayawa takara a karo na uku," in ji mai magana da yawun jam'iyyar.

Ya kara da cewa, “Da farko dai jam’iyyar ta so yin shiru a kan shi, amma kuma akwai matukar amfani idan ta tura mishi sako gamsasshe tare da sauran mutane masu irin tunaninsa.”

“A taron shuwagabannin jam’iyyar da ya gabata, shugaban kasa Buhari ya tabbatar da cewa, zai bi yadda tsarin kundin mulki ya tanada kuma zai kiyaye rantsuwarsa da yayi da Al-Qur’ani.” In ji mai magana da yawun jam’iyyar APC, Lanre Issa-Onilu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel