PDP ta yi ma INEC wankin babban bargo, ta nemi Mahmud Yakubu ya yi murabus

PDP ta yi ma INEC wankin babban bargo, ta nemi Mahmud Yakubu ya yi murabus

Uwar jam’iyyar PDP ta yi ma hukumar INEC kaca kaca tare da yin kira ga shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu da ya yi murabus sakamakon zargin yin kutse cikin na’urar zabe na Card Reader kafin zaben jahar Kogi da Bayelsa.

Kaakakin jam’iyyar PDP, Kola Ologbondiyan ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, inda yace tabbacin fitowar wannan magana da daga bakin daraktan watsa labaru da wayar da kan masu zabe na hukumar INEC, Festus Okoye kadai ya isa hujja a wajensu, wanda ke tabbatar da magudin zabe a zabukan biyu.

KU KARANTA: Madallah: Sheikh Minista Pantami ya hana shugaba Buhari gaisawa da mata

Jaridar Punch ta ruwaito a ranar Laraba ne Okoye ya tabbatar da cewa an yi kutse a na’urar card reader, don haka na’aurar ta rage karsashi kuma ba za ta taba samar da sakamakon da ake bukata daga wajenta na tsaftace zabe ba.

“Tabbacin wannan matsala daga bakunan manyan jami’an INEC bai zo mana da mamaki ba, asali ma dai ya kara jaddada zargin da muke yi na cewa an tafka magudin zabe a zabukan biyu, kuma wannan ya tabbatar da cewa INEC bata da wani kariya a gaban kotu sakamakon bambamcin alkalumman sakamakon zabe da aka samu a sakamakon zaben 2019 da ta sanar.” Inji kaakakin PDP.

Kaakakin yace lokaci yayi a shugaban hukumar INEC, Mahmud Yakubu zai yi murabus daga mukaminsa, saboda abin kunya ne INEC ta fada ma yan Najeriya cewa sai a yanzu ne ta fahimci na’urar tantance katin zabe na da matsala, bayan wasu sun yi amfani dasu wajen magudin zabe.

Sai dai duk wannan matsala da INEC ta tabbatar dake tattare da Card Reader, hukumar tace hakan ba yana nufin zata daina amfani da na’aurar bane a zabuka masu zuwa kamar yadda Festus Okoye ya tabbatar.

A wani labarin kuma, hukumar INEC za ta gudanar da zaben karashe a mazabar Sanatoriya ta Kogi ta yamma a jahar Kogi da kuma mazabar Sabuwa ta jahar Katsina, a ranar Asabar, 30 ga watan Nuwamba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel