Sunaye da ma'aikatu: El-Rufai ya sake nada kwamishinoni mata biyu a Kaduna

Sunaye da ma'aikatu: El-Rufai ya sake nada kwamishinoni mata biyu a Kaduna

Majalisar jihar kaduna a ranar Alhamis ta tabbatar da nadin wasu kwamishinoni mata biyu. Majalisar ta kuma tabbatar da nadin mamba na hukumar sa ido kan yadda ake kashe kudade na jihar.

An tabbatar da su ne sakamakon wasikar da mukadashin gwamnan jihar, Dakta Balarabe Hadiza ta aike wa majalisar kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Wadanda aka tabbatar din sun hada da Dakra Amina Baloni a matsayin kwamishinan lafiya da Hajiya Halima Lawal a matsayin kwamishinan ayyukan noma yayin da Muhammad Sada Jalal aka nada shi mamba a hukumar saka ido kan yadda ake kashe kudade a jihar.

Kakakin majalsar, Alhaji Aminu Shagali ne ya jagoranci zaman majalisar tare da tantance wadanda aka yi wa nadin.

DUBA WANNAN: 'Yan siyasa 3 da PDP za ta iya tsayarwa takara idan tana son karbe mulki a 2023

Wadanda aka tantance din sun bayar da takaitacen tarihinsu sannan daga bisani aka ce suyi gaisuwa su tafi.

Kazalika, Kudirin dokar hada asusun jiha da na kananan hukumomi ta 2019 da na Ayyukan ma'aikatan gwamnati na 2019 sun samu shiga a majalisar inda suce wuce karatun farko da na biyu.

An mika kudirin dokar na farko ga kwamitin kananan hukumomi da ayyukan walwalar alumma, kudi da sharia yayin da kudin na biyu an mika shi ga kwamitin ilimi, shari'a da ayyuka na musamman domin su dauki matakin da ya dace a kansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel