Abinda ya hana mu soken zaben Bayelsa da Kogi - INEC ta magantu

Abinda ya hana mu soken zaben Bayelsa da Kogi - INEC ta magantu

- Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana abubuwan da suka dakatar da ita daga soke zaben da aka gudanar a jihar Bayelsa da Kogi

- Kwamishina a INEC, Festus Okoye, ya ce dokokin zabe da kotuna sun matukar rage wa hukumarsu katabus

- Okoye ya lissafa wasu daga cikin manyan kalubalen da INEC ke fuskanta a kokarinta na sauke nauyin da ya rataya a wuyanta

Kusan mako guda bayan kammala zaben gwamna a jihohin Bayelsa da Kogi, hukumar INEC ta bayyana dalilin da yasa bata soke zaben da aka gudanar a jihohin ba duk da irin rigingimu da aka ce sun faru a ranar da aka gudanar da zabukan.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta dora alhakin gazawarta a kan yanayin dokokin Najeriya.

INEC ta bayyana cewa dokokin Najeriya basu bata damar soke sakamakon zabe ba kamar yadda jama'a da 'yan sa ido ke kiran ta yi ba.

Hukumar zaben ta bayyana hakan ne yayin wani taro da ta gudanar da wasu kungiyoyi a Abuja, inda ta bayyana cewa sashe na 26 na kundin tsarin mulki ne kadai ya iya bawa INEC hurumin daga zabe.

DUBA WANNAN: Dino Melaye ya roki INEC da ta dage zaben Kogi ta Yamma, ya bada dalili

"Babu wata doka da ta bawa hukumar zabe ikon soke zabe, hatta 'yan majalisa da suke kiran mu soke zabe, sun dogara ne da sashe na 26 na kundin tsarin mulki, wanda ya bawa INEC ikon daga zabe, amma ba soke zaben da aka riga aka fara ko aka kammala ba," a cewar Festus Okoye, kwamishina a hukumar INEC.

Okoye ya kara da cewa hatta kotuna, da suka hada da kotun koli, sun sha yanke hukuncin cewa hukumar INEC bata da ikon soke sakamakon zabe da baturen zabe ya riga ya bayyana sakamakonsa a matakin mazaba.

A cewar Okoye, akwai bukatar masu ilimi da jagorori a kowanne mataki su rungumi tsarin siyasar gaskiya a matsayin tafarkin dimokradiyya, matukar ana son hukumar zabe ta iya gudanar da sahihin zabe da za a yaba mata, ta sauke nauyin da ke kanta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel