Garambawul: Majalisa ta yankewa masu garkuwa hukuncin daurin rai

Garambawul: Majalisa ta yankewa masu garkuwa hukuncin daurin rai

A karshe, Majalisar Dattawan kasar nan ta yi wa dokokin laifuffuka garambawul inda ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga duk wanda aka samu da laifin garkuwa da mutane a Najeriya.

Kamar yadda mu ka samu labari, Majalisar ta kawo kudirin daurin rai ne ga masu sace jama'a, domin maye gurbin dokar da ake amfani da ita a halin yanzu wanda ta yanke daurin shekaru 10.

Sanata Oluremi Tinubu mai wakiltar Legas ta tsakiya a majalisar dattawa ta gabatar da wannan kudiri. Wannan kudiri idan ya zama doka zai canji hukuncin daurin shekaru 10 da ake yi a kaso.

Haka zalika idan an rattaba hannu a kan wannan kudiri, za ayi wa hukuncin da aka tanada ga wadanda aka samu da laifin fyade kwaskwarima bayan an yi wa dokokin laifuffuka garambawul.

KU KARANTA: An daure Tsohon Kwamishinan Jihar Zamfara da zargin satar mutane

Sanatar ta jam’iyyar APC, Remi Tinubu ta bayyana cewa yawan sace mutane da ake yi ana garkuwa da su a fadin kasar nan ya sa ta jawo wannan kudiri da zai sake duba dokokin Najeriyar.

Tinubu ta ce a dalilin garkuwa da mutane da ake yi, mutane da yawa sun shiga cikin mawuyacin hali. ‘Yar majalisar ta ce wannan kudiri zai taimaka wajen maganin masu aikata wannan laifi.

Don haka wannan kudiri ya tanadi dauri ga wanda aka samu da laifin garkuwa da mutane. Inji Sanatar. Wannan zai zama hukuncin da ya dace da masu aikatawa ko shirin aikata mugun laifin.

Kwaskwarimar ta kuma shafi yi wa sashe na 221 na dokokin kasa garambawul inda aka ce duk wanda ya kwanta da mai karancin shekaru ko tabin kwakwalwa zai yi zaman kason shekaru 2.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel