Rufe iyakokoki na mana mummunar illa: Wasu sarakunan Najeriya sun koka

Rufe iyakokoki na mana mummunar illa: Wasu sarakunan Najeriya sun koka

Sarakunan gargajiya kuma mazauna yankin garuruwan iyakokin Najeriya a jihar Ogun, sun koka a kan kalubalen da suke fuskanta na rufe iyakokin, sunce "sabuwar dokar na kashesu".

Sarakunan gargajiya shida da suka hada da, Onihunbo na masarautar Ihunba, Sarki Joseph Adesiyan, sanannen masanin tarihi; Farfesa Anthony Asiwaju da wasu mazauna yankin masu yawa, sun ce kwashe amfanin gona da kayan kiwonsu na gagara saboda yadda masu tsaron iyakokin ke hantararsu da sunan kayayyakinsu na sumogal ne.

A yayin tattaunawa da manema labarai a Abeokuta babban birnin jihar, zauren shuwagabannin garuruwan da ke da iyakoki a jihar Ogun da sauran masu ruwa da tsaki, sun yi kira ga shugaba Buhari da ya kara duba dokar rufe iyakokokin.

Sun kara da kira ga shugaba Buhari da ya duba dokar hana kai man fetur garuruwan da ke da nisan kilomita 20 kusa da iyakokin. Sun jajanta yadda jami'an hukumar kwastam ta kasa suka tsawwala musu rayuwa ta hanyar fakewa da dokar fadar shugaban kasar ta hana kai man fetur yankunan.

DUBA WANNAN: 'Yan siyasa 3 da PDP za ta iya tsayarwa takara idan tana son karbe mulki a 2023

Mai magana da yawun zauren shuwagabannin, ya ce haramta kai man fetur din ya kawo matsi na rayuwa ga garuruwan, tare da mutanen da basu da laifin zagon kasa ga tattalin arzikin kasar nan ta hanyar sumogal.

Asiwaju ya jajanta cewa, dokar shugaban kasar ta tada hankulan mutanen yankin masu tsananin bin dokar kasa. Ta kara da kawo matsi na tattalin arziki ga mutanen yankin.

A don haka ne, jama'ar yankunan ke mika koke tare da roko ga gwamnatin tarayya, da ta janye dokar rufe iyakokin da hana kai man fetur yankunan, kafin hakan ya yi nasarar karar da mutanen yankunan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel