Gabatar da takardar NYSC ta bogi: Kotu ta bayar da umarnin kama mamba a majalisar dattijai

Gabatar da takardar NYSC ta bogi: Kotu ta bayar da umarnin kama mamba a majalisar dattijai

- Wata kotu da ke zamnta a unguwar Lugbe a Abuja ta bayar da umarnin kama Sanata Lawrence Ewhrudjakpo saboda kin bayyana a gabanta duk da aika masa sammaci

- Ana zargin Sanata Ewhrudjakpo da gabatar da takardar kammala bautar kasa (NYSC) ta bogi lokacin da ya cike takardun INEC domin tsaya wa takara

- Mai kara, Youdiowei, ya yi ikirarin cewa har yanzu dan majalisr yana amfani da takardar bogin a cikin takardunsa na karatu

A ranar Laraba ne wata kotun Abuja da ke zamanta a Lugbe ta bayar da umarnin kamo mata mamba a majalisar dattijai mai wakiltar mazabar jihar Bayelsa ta yamma, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo, saboda kin mutunta sammacin kotun.

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa alkalin kotun ne ya bayar da umarnin kama Sanata Ewhrujadkpo saboda ya gaza bayyana a gaban kotun domin fuskantar tuhumar da ake yi masa ta amfani da takardar kammala bautar kasa (NYSC) ta bogi.

Benjamin Youdiowei, wani jigo a jam'iyyar APC, shine ya shigar da karar karar sanata Ewhrujadkpo tun kafin a gudanar da zabe.

Youdiowei na zargin Sanatan da mika takardar NYSC ta bogi a cikin takardunsa na tsaya wa takara da ya mika wa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).

Mai karar ya yi zargin cewa har yanzu dan majalisar yana tare da takardar bogin kuma yana amfani da ita a cikin jerin takardunsa na karatu.

DUBA WANNAN: Gwamnonin APC 3 da kan iya gadar Buhari a 2023

Yayin zaman kotun na ranar Laraba, 27 ga watan Nuwamba, mai karar ya nuna damuwarsa a kan yadda wanda ake kara ya cigaba da kaurace wa kotun duk da an aika masa da sammaci ba sau daya ba.

Sai dai, lauyan da ke kare Sanatan ya bawa kotun hakuri bisa rashin bayyanar wanda ake kara tare da bayyana cewa dan majalisar ya yi bulaguro ne zuwa wani wuri mai nisa daga inda kotun ke zamanta.

Lauyan ya roki kotun ta sake sake bawa Sanatan dama ta hanyar sake saka masa wata ranar da zai bayyana a gabanta.

Amma, lauyan da ke wakiltar me kara ya soki bukatar lauyan wanda ake kara, lamarin da yasa alkalin kotun, Abubakar Sadiq, ya bayar da umarnin a kamo Sanatan don tilasta shi gurfanar a gaban kotun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel