Liyafar N30: Yadda wani sabon wajen cin abinci ya hana almajirai bara

Liyafar N30: Yadda wani sabon wajen cin abinci ya hana almajirai bara

- A kwanakin baya ne ministan harkokin noma, Sabo Nanono, ya bayyana cewa N30 ta isa mutum ya ci abinci ya koshi a Kano

- Kalaman ministan sun jawo cece-kuce, hakan kuma yasa wani mutum ya bude gidan sayar da abinci na N30 a Kano

- Mazauna garin Kano sun bayyana cewa sabon gidan abincin yasa yawan barar da almajirai ke yi a Kan ya ragu saboda gidan abincin

A unguwar Sani Mainagge,sakamakon sake bude gidan abinci na Naira talatin gidaje dake makwabtaka da gurin sun fara sauke tukwanansu.

Biyo bayan maganar da minstan noma Alhaji Sabo Nanono yayi, a game da abincin Naira talatin, wanda sakamakon hakan ya saka aka bude gidan abincin a unguwar Sani Mai Nagge.

Sai ga shi wani mai gyaran Rediyo ya samu karfin giwa inda shi ma ya bude gidan abincin na Naira 30.

Wanda ya bude gidan ya shaidawa Freedom Radio cewa sakamakon bude gidan abincin na Naira talatin makotansa sun sauke tukwane saboda saukin abincin sa.

Haruna Injinya ya kara da cewa makotan nasa kan turo yara biyar da Naira dari da hamsin domin sayan abinci.

DUBA WANNAN: Dino Melaye ya roki INEC da ta dage zaben Kogi ta Yamma, ya bada dalili

Haruna mai sabon gidan abincin na Naira 30 ya kara da cewa a rana yana dafa shinkafa buhu daya da wake rabin buhu da garin kwaki buhu daya.

Ya kara da cewa wasu na zuwa gidan abincin domin saye a rabawa mabukata.

A nata bangaren mai dakin da ya bude sabon gidan abincin Hajiya Sadiya Saidu ,ta ce hatta Almajiran unguwar na zuwa sayan abincin na Naira talatin.

Ta kara da cewa hakan ta sa Almajiran sun daina bara sai dai su nemo Naira talatin domin sayan abincin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel