Shugaban kasa Buhari zai shilla kasar Equatorial Guinea daga nan zai wuce Daura

Shugaban kasa Buhari zai shilla kasar Equatorial Guinea daga nan zai wuce Daura

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tafi kasar Equatorial Guinea domin halartar taron kasashe masu fitar da iskar gas a kasuwannin duniya karo na biyar da zai gudana a babban birnin kasar, Malabo.

Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, wanda ya bayyana cewa taron na kwana daya zai samu halartar manyan kasashe masu fitar da iskar gas kamar Algeria, Egypt, Libya, Bolivia, Iran, Qatar, Rasha, UAE, Norwa, Kazakhstan, Venezuela da Trinidad & Tobago.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Bututun iskar gas ta fashe a jahar Legas, ta kashe mutane 4, 50 sun jikkata

A shekarar 2001 aka fara kirkirar wannan taro a yayin taron ministoci da aka yi a kasar Iran, yayin da taron farko na kasashe masu arzikin iskar gas ya gudana a birnin Doha na kasar Qatar a shekarar 2011, na uku an yi shi a Iran a 2015 wanda Buhari ya halarta, wannan ne karo na farko da za’a yi a Afirka.

A taron shekarar 2015, shugaban kasa Buhari ya bayyana ma mahalarta taron cewa: “Najeriya ta fi karfi wajen fitar da iskar fiye da danyen mai, wannan dadadden lamari ne da aka tabbatar. Da ace an cigaba da tafiyar da tsarin da aka shimfida ma bangaren iskar gas a shekarun 1970 da mun samu cigaba sosai a fannin.”

“Najeriya ce kasa ta 1 dake da arzikin iskar gas a nahiyar Afirka gaba daya, yayin da ta kasance kasa ta 9 mai arzikin iskar gas a duniya, don haka Buhari zai jaddada ma taron manufar Najeriya na ganin an baiwa kowacce kasa damar sarrafa iskarta ta yadda zai amfani jama’anta ba tare da cutar da muhallinta ba.” Inji Garba.

Daga cikin yan rakiyar shugaba Buhari akwai ministan harkokin kasashen waje Geoffrey Onyeama, ministan man fetir, Timipre Sylva, ministan tama da karafa, Olamilekan Adegbite da shugaban hukumar NNPC, Mele Kyari.

Malam Garba Shehu ya karkare sanarwar da bayyana cewa daga Malabo shugaba Buhari zai zarce kai tsaye zuwa garin Daura na jahar Katsina inda zai yi hutun kwana 5.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel