Da dumi dumi: Bututun iskar gas ta fashe a jahar Legas, ta kashe mutane 4, 50 sun jikkata

Da dumi dumi: Bututun iskar gas ta fashe a jahar Legas, ta kashe mutane 4, 50 sun jikkata

Akalla mutane hudu ne suka mutu a sanadiyyar fashewar wata bututun iskar gas dake unguwar Aduke, cikin karamar hukumar Ifelodun na jahar Legas, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan ibtila’I ya faru ne da sanyin safiyar Alhamis, 28 ga watan Nuwamba, inda baya ga halaka mutane hudu, akalla mutane 50 kuma sun samu munanan rauni a sanadiyyar gobarar.

KU KARANTA: Mai alfarma Sarkin Musulmi ya bayyana yau a matsayin 1 ga watan Rabiul -Thani

Rahotanni sun bayyana cewa daga cikin mutanen da suka mutu akwai kananan yara guda biyu. Sai dai shugaban hukumar bada agajin gaggawa na jahar Legas, LASEMA, Olufemi Oke-Osanyintolu ya bayyana cewa mutane 23 ne suka jikkata.

Mista Olufemi yace sun kwashe mutanen da suka kone a sanadiyyar gobarar zuwa babban asibitin Gbagada domin samun kulawa, inda ya kara da cewa akwai mutane biyar da suka hada da kananan yara 3 da mata 2 da suka gobarar ta fi shafa.

Shugaban LASEMA yace: “Bincike ya nuna gobarar ta tashi ne a sanadiyyar kiran waya da wani mutumi ya yi, daga nan ne wutar ta shiga shagunan dake kusa da bututun da kuma wani gida dake bayan shagunan, sai dai yara biyu sun mutu.

“Haka zalika mun gano gawar wata mata mai suna Damilare Afolabi, wanda tuni muka kwashe gawarta muka mika ma iyalanta, a yanzu dai mun kewaye yankin don gudun kada wani ya shiga.” Inji shi.

Daga karshe shugaban yace akwai bukatar rushe duk gine ginen da gobarar ta shafa domin gudun faduwarsa a nan gaba.

A wani labarin kuma, majalisar zartarwar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta amince da kashe naira biliyan 19 domin ginin wasu manyan hanyoyi a jahar Kano, jahar Oyo da kuma babban birnin tarayya Abuja.

Ministan ayyuka, Babatunde Raji Fashola ne ya sanar da haka yayin da yake ganawa da manema labaru bayan kammala taron majalisar a ranar Laraba, 27 ga watan Nuwamba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel