Gwamnan Bayelsa ya shirya ma sabon gwamna mai jigan gado tarkon rago

Gwamnan Bayelsa ya shirya ma sabon gwamna mai jigan gado tarkon rago

Wata kungiya mai zaman kanta dake rajin tabbatar da shugabanci na gari a jahar Bayelsa ta bayyana cewa gwamnan jahar mai barin gado, Seriake Dickson ya shirya ma gwamna mai jiran gado, David Lyon ramin mugunta, don haka take gargadin sabon gwamnan.

Kungiyar mai suna Bayelsa Rainbow Coalition for Good Governance ta shawarci sabon zababben gwamnan jahar, David ya yi takatsantsan da duk wasu matakai da Gwamna Dickson zai dauka a yan kwanakin suka rage masa a karagar mulki, domin kada ya fada tuggunsa.

KU KARANTA: Mai alfarma Sarkin Musulmi ya bayyana yau a matsayin 1 ga watan Rabiul -Thani

Shugaban kungiyar, Barista Francis Wainwei ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru a garin Yenagoa na jahar Bayelsa a ranar Talata, inda yace yawancin mutanen da Dickson ya nada mukaman manyan sakatarori a ma’aikatun jahar Bayelsa basu cancanta ba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito a ranar juma’ar da ta gabata ne gwamnan ya nada sabbin manyan sakatarori guda 35, tare da sabon kwamishina guda 1, duk da cewa yawancin al’ummar jahar sun soki wadannan nade nade.

Kungiyar ta bayyana cewa manufar Gwamna Dickson na yin wadannan ande nade ba wai don kyautata ma al’ummar jahar Bayelsa bane, a’a, sai dai don ya gadar ma gwamnati mai zuwa tsabar zambar kudi da za ta dinga kashewa a dalilin sabbin nade naden.

A wani labarin kuma, kotun daukaka kara dake zamanta a babban birnin tarayya Abuja ta yi fatali da karar da jam’iyyar APC ta mika mata game da korafin da take da shi game da zaben gwamnan jahar Benuwe Samuel Ortom, inda take kalubalantar nasarar daya samu.

Da take yanke hukuncinta, kotun, ta bakin babban Alkali, Mai sharia Fred Oho ya bayyana cewa kotu ta yi watsi da korafe korafen jam’iyyar APC sakamakon basu da tushe balle makama, saboda jam’iyyar da dan takararta sun gaza gamsar da kotu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel