To fah: Budurwa ta kashe kanta awanni kadan bayan saurayinta yayi hatsari ya mutu

To fah: Budurwa ta kashe kanta awanni kadan bayan saurayinta yayi hatsari ya mutu

- Bacin rai da tashin hankali ne yasa wata budurwa kashe kanta bayan mutuwar saurayinta

- Mota ce ta take saurayin nata mai suna Jason, wanda ya mutu bayan an mika shi asibiti

- Alice ta yanke shawarar kashe kanta ne bayan da ta tura mishi sakon karta kwana ta wayarshi

Bacin rai da kuncin rayuwa suka sa wata mata ta kashe kanta bayan sa’o’I kadan da wani direba ya take saurayinta ya mutu.

Alice mai shekaru 26 ta kashe kanta ne bayan da ta turawa mamacin saurayin nata sakon karta kwana ta wayarshi, cewa ba zata iya rayuwa babu shi ba.

Wajen karfe 8 na dare a ranar 22 ga watan Disamba 2018, wata mota ta taka Jason Francis. Bayan an sanar da Alice abinda ya faru, a take ta fadi a gaban ‘yan sanda.

Bayan sa’a daya da mutuwarshi, ta tura mishi sakon cewa tana sonshi kuma zata biyo shi.

Bayan da Alice ta mutu, iyayenta sun je asibitin Royal Perth tare da ce musu, da basu bar Alice ta bar asibitin ba bayan da aka sanar da ita mutuwar saurayinta.

KU KARANTA: An caccaki mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna akan ta dauki hoto da Mufti Menk ba tare da ta rufe kirjinta ba

Iyayenta sun ce: “Alice kyakyawa ce mai hazaka. Ko a lokacin da ta koma Australia tare da Jason, mun yi bakin ciki. Amma munsan zasu rayu cikin soyayya da kaunar juna tare. Duk wanda ya sansu, zai yi sha’awar irin rayuwar da suke yi tare.”

Sun kara da cewa, “A ranar 22 ga watan Disambar shekarar da ta gabata, hankulanmu sun tashi bayan da muka samu labarin mutuwar Jason. Bayan sa’o’I kadan sai aka sanar mana da mutuwar Alice.”

“Za a iya gujewa mutuwar Alice ta hanyar hanata fita daga asibitin bayan da Jason ya rasu. Yadda ta fadi bayan da aka sanar mata da lamarin, ya bayyana irin kaunar da take mishi.” suka kara da cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel