An caccaki mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna akan ta dauki hoto da Mufti Menk ba tare da ta rufe kirjinta ba

An caccaki mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna akan ta dauki hoto da Mufti Menk ba tare da ta rufe kirjinta ba

- Wani mutum ya caccaki mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Dr. Hadiza Balarabe

- Ya zargeta da rashin rufe kirjinta a cikin jama’a wadanda ba muharramanta ba

- Mutumin ya yi maganar ne bayan da mataimakiyar gwamnan ta wallafa hotunan data dauka da fitaccen malamin addinin musuluncin nan na duniya Mufti Menk

Wani mutumi ya caccaki mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Dr. Hadiza Balarabe a kan rashin rufe kirjinta da kyau lokacin da ta dauki hoto da fitaccen Malamin addinin Musuluncin nan na duniya Mufti Isma'il Menk.

Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe, mataimkaiyar gwamnan jihar Kaduna, ta fuskanci kalubale daga wani Musulmi a kafar sada zumunta, a kan rashin rufe kirjinta da bata yi ba.

Mataimakiyar gwamnan ta karba bakuncin wani malamin musulunci ne. Tana sanye da kayan hausawa tare da babban mayafi. Amma hakan bai sa saurayin ya kyaleta ba ba tare da ya caccake ta ba.

KU KARANTA: Tirkashi: Miji ya bayyana yadda ya kama matarshi tana lalata da dan uwanshi na jini

Ta wallafa tare da hotuna a shafinta na tuwita: “Da yammacin nan, na karbi sanannen malamin musulunci Mufti Isma’il Menk. Malamin ya kasance mai wa’azi tare da nasihohin ga miliyoyin mutane da ke fadin duniyar nan.”

Mutumin mai suna Musa Yusuf Ubandoma, ya je kasan hotunan da rubutun yake, inda ya wallafa rubutunshi kamar haka: “Amma me hakan ke nunawa? Cewa ke ba mata ko uwa musulma ta gari ba ce? A cikin mutanen da ba muharramanki ba kin kasa rufe kirjinki. Tunatarwa ce kawai nake miki. Ubangiji ya yafe mana zunubbanmu.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel