Naira dubu dari bakwai ake biyana fansho duk watan duniya - Tsohon gwamna

Naira dubu dari bakwai ake biyana fansho duk watan duniya - Tsohon gwamna

- Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Balarabe Musa ya bayyana nawa gwamnatin jihar Kaduna ke biyanshi a matsayin kudin fansho

- Tsohon gwamnan ya bayyana cewa, shi da sauran tsoffin gwamnonin jihar sun aminta da kudin fansho dai-dai da na manyan sakatarorin gwamnatin jihar

- Jihohin Legas, Gombe, Bauchi, Akwa-Ibom, Kwara, Kano da Ribas na sahun gaba wajen ba tsoffin gwamnoninsu kudin alawus na musamman

Har yanzu dai ana cigaba da cece-kuce a kan dokar biyan tsofaffin gwamnoni kudin fansho ko alawus na musamman na daruruwan miliyoyin naira.

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Balarabe Musa ya ce N742,000 ake biyanshi fansho a matsayinshi na tsohon gwamnan jihar Kaduna.

Yace tsoffin gwamnonin jihar Kaduna sun amince da karbar kudin fansho dai-dai da yadda manyan sakatarorin gwamnatin jihar ke karba.

Lamarin ya ja hankulan mutane ne bayan da tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari ya nemi gwamnatin jiharshi da ta biya shi naira miliyan 10 a kowanne wata a matsayin alawus na musamman, kamar dai yadda dokar gwamnatin jihar ta tanadar.

A ranar Talata ne majalisar dokokin jihar ta soke wannan dokar. Tana mai cewa, tsoffin gwamnonin jihar kafinshi sun shafe shekaru ba a biyansu kudaden a yayin shekaru 8 na mulkinshi.

KU KARANTA: Abin mamaki: Likita ya ciro kifi mai rai a hancin wani yaro

Wasu masana na ganin bai kamata a cigaba da biyan tsoffin gwamnonin wadannan makuden kudin ba, duba da halin da kasar nan take ciki.

Wasu masanan kuwa suna ganin fansho na wadanda suka yi aikin gwamnati na tsawon rayuwarsu ne, ba wai ‘yan siyasa ba.

Jihohin Legas, Gombe, Bauchi, Akwa-Ibom,Kwara, Kano da Ribas na sahun gaba wajen ba tsoffin gwamnoninsu kudin alawus na musamman.

Ana biyan tsoffin gwamnonin daga naira miliyan 200 zuwa 300 ko fiye da hakan. Ana kuma kula da lafiyarsu da samar musu gida a Abuja da jiharsu. Ana sabunta musu motocin hawa bayan shekaru 3 zuwa 4 ko kuma biyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel