Yanzu yanzu: Kotu ta tabbatar da nasarar gwamnan PDP a kan jam’iyyar APC

Yanzu yanzu: Kotu ta tabbatar da nasarar gwamnan PDP a kan jam’iyyar APC

Kotun daukaka kara dake zamanta a babban birnin tarayya Abuja ta yi fatali da karar da jam’iyyar APC ta mika mata game da korafin da take da shi game da zaben gwamnan jahar Benuwe Samuel Ortom, inda take kalubalantar nasarar daya samu.

Da take yanke hukuncinta, shugaban Alkalan kotun, Mai sharia Fred Oho ya bayyana cewa kotu ta yi watsi da korafe korafen jam’iyyar APC sakamakon basu da tushe balle makama, saboda jam’iyyar da dan takararta sun gaza gamsar da kotu.

KU KARANTA: Cika shekaru 60 a rayuwa: Buhari ya yi ma Garba Shehu kyakkyawar shaida

Jaridar Daily Trust ta ruwaito baya ga fatali da bukatar ta, haka zalika kotun daukaka kara ta sanya ma jam’iyyar APC taran kudi naira 150,000 saboda bata mata lokaci.

A nasa bangaren kuma, gwamna mai nasara, Gwamna Samuel Ortom ya bayyana cewa ya sadaukar da nasarar daya samu a gaban kotu ga al’ummar jahar Benuwe wanda yace su ne suka sake zabensa karo na biyu.

Ortom ya bayyana haka ne ta bakin mai magana da yawunsa, Terver Akase, inda yace hukuncin kotun daukaka karan ya yi daidai da hukuncin da kotun sauraron koke koken zabe ta yanke, wanda kuma shine ya yi daidai da ra’ayin jama’an Benuwe a zaben 2019.

“Gwamnan ya bayyana godiyarsa ga uwar jam’iyyar PDP da mambobinta bisa goyon bayan da suka bashi, sa’annan yana jinjina ma lauyoyinsa bisa kokarin da suka tare da jajircewar da suka nuna wajen wannan sharia.” Inji kaakakin.

Daga karshe gwamnan ya yi kira ga jam’iyyar APC, da dan takararta Emmanuel Jime dasu hada hannu da shi domin ciyar da jahar Benuwe gaba.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jinjina ma babban hadiminsa a kan harkokin kafafen watsa labaru, kuma mai magana da yawunsa, watau kaakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu yayin daya cika shekaru 60 a rayuwa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel