Buhari ya nemi amincewar majalisa don karbo bashin $30bn da aka hana shi karba zamanin Saraki

Buhari ya nemi amincewar majalisa don karbo bashin $30bn da aka hana shi karba zamanin Saraki

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, ya bukaci majalisar tarayya da ta aminta da karbo bashin $29.96 don aiwatar da manyan aiyukan more rayuwa a fadin kasar nan. Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ne ya karanto wasikar a zaman zauren majalisar.

A wasikar, Buhari ya ce, ya yanke hukuncin turo bukatar aron $29.96 ga majalisar. Wannan na daga cikin bukatar da majalisar tarayya ta 8 ta ki karba.

Wasikar mai taken: "Bukatar ga majalisar tarayya a kan ta kara dubawa da kuma aminta da tsarin karbo bashi na 2016-2018".

"Don yin biyayya ga sashi na 21 da 27 na hukumar bashi, ina mika wannan bukata ta tsarin aro kudi don aiwatar da manyan aiyuka. Na tura irin wannan bukatar ga majalisar dattawan kasar nan amma basu amince ba." takardar ta bayyana.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: An gurfanar da wani tsohon sanata da tsohon kakakin majalisa gaban kotu

"Wannan tsarin da kuma aiyukan da za a aiwatar da wannan bashin zasu taka rawar gani wajen cigaba a manyan bangarori irinsu wutar lantarki, tituna, noma da kiwo, lafiya, ruwan sha da bangaren ilimi." Kamar yadda takardar ta sanar

Takardar ta kara da cewa,"Kamar yadda ya dace, na zo neman yardarku. Bayanan da suka danganci wannan tsarin zasu fito daga wajen ministar kudi don amicewarku,"

"Na umarci ministar da ta zamo a shirye kowanne lokaci don samar da karin bayani ko karin haske da zai sa ku amince da bukatar da gaggawa." inji takarda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel