Kisan dan sanda da dan jarida: An gurfanar da yan Shi'a 60 a Abuja

Kisan dan sanda da dan jarida: An gurfanar da yan Shi'a 60 a Abuja

Hukumar yan sanda a ranar Laraba ta gurfanar da yan Shi'a 60 kan laifin kisan kai, tayar da zaune tsaye, lalata dukiyoyin al'umma da kuma tayar da tarzoma

Matasan da aka tsare bayan zanga-zangan da suka gudanar ranar 22 ga Yuli, 2019 a Abuja sun gurfana gaban babban kotun birnin tarayyar Abuja.

Bayan karanto musu laifukan da ake zarginsu da shi da yaren Turanci da Hausa, sun musanta aikata laifukan.

Zanga-zangar da suka gudanar ya yi sanadiyar mutuwan babban jami'in yan sanda, DCP Usman Umar da dan bautan kasa kuma dan jarida, Precious Owolabi, inda rikici ya barkke tsakanin yan sanda da yan Shi'a.

DUBA NAN Yan Boko Haram sun kai hari jihar Yobe

Bayan sun musanta wannan zargi, lauyan yan sanda, Simon Lough ya bukaci a garkamesu a kurkukun Kuje.

Hakazalika ya bukaci kotun ta koma zama kurkukun Kuje saboda wahalan kawo yan Shi'an 60 kotu duk ranan da aka bukacesu.

Lauyan yan Shi'a , Bala Dakum, bai yi jayayya kan haka ba.

Amma ya bayyanawa kotu cewa yana bukatan kotun ta basu beli. Alkali mai shari'a, Sulaiman Belgore, ya ce a cigaba da garkamesu a ofishin hukumar SARS zuwa ranar 10 ga Disamba da za'a cigaba da saurarin karar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel