Yan Boko Haram sun kai hari jihar Yobe

Yan Boko Haram sun kai hari jihar Yobe

Wasu yan ta'addan Boko Haram sun kai hari Babban Gida, hedkwatan karamar hukumar Tarmuwa ta jihar Yobe a ranar Laraba, 27 ga Nuwamba, 2019.

Wani mazaunin Babban Gida, Alhaji Gidado, ya ce yan ta'addan sun fara kai hari mazaunin jami'an Soji kafin suka karasa wuraren ajiyan kayan abinci sukayi awon gaba da su.

Kwamishanan yan sandan jihar Yobe, Abubakar Sahabu, ya tabbatar da labarin inda yace DPO na Babban Gida ya laburta masa.

Yace: "DPO na ya kirani domin sanar da ni cewa wasu yan Boko Haram sanye da kayan Sojoji sun dira Babban gida, hedkwatar karamar hukumar Tarmuwa cikin motoci kirar Toyota Hilux 9 suna harbin kan mai uwa da wabi."

"Na sanar da jami'an Sojojin da ke filin daga."

Kwamishanan ya kara da cewa kurar ta kwanta yanzu kuma an daina harbe-harben.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel