Yanzu-yanzu: An gurfanar da wani tsohon sanata da tsohon kakakin majalisa gaban kotu

Yanzu-yanzu: An gurfanar da wani tsohon sanata da tsohon kakakin majalisa gaban kotu

- Wani tsohon sanata daga jihar Ebonyi, Emmanuel Onwe ya gurfana a gaban kotun laifuka na musamman

- A tare dashi akwai kakakin majalisar jihar Bayelsa tare da wasu mutane hudu a kan amfani da kujerarsu ba ta yadda ya dace ba

- Dukkan wadanda ake zargin sun musanta aikata laifukan da ake tuhumarsu da su

Wani tsohon sanata, Emmanuel Onwe daga jihar Ebonyi, tsohon kakakin majalisar jihar Bayelsa, Friday Komboyein da wasu mutane hudu an gurafanar da su gaban kotun manyan laifuka ta musamman a Abuja, a kan zarginsu da ake da karantsaye ga dokokin aiyukan gwamnati.

Wata takardar da kakakin kotun laifuka na musamman, Ibraheem Zakariya ya fitar, ya ce an gurfanar da tsohon kwamishinan jihar Ebonyi ne sakamakon kin mika takardar bayyana kadarorinshi a lokacin da ya dace. An gurfanar da Komboyein ne da sauran a kan zarginsu da ake da amfani da kujerarsu ba ta yadda ya kamata ba.

DUBA WANNAN: Tirkashi: An cafke wata mata dauke da ATM 23 boye a 'gabanta'

Wadanda aka gurfanar tare da kakakin majalisar sun hada da tsoffin magatakardar majalisar –Aaron Timiye da Owudogu Edward, tare da wasu tsoffin akawun majalisar har su biyu – Thomas Tamaraodubo da Koroye Stephen.

Kamar yadda Zakariya ya ce, dukkan wadanda aka gurfanar din sun musanta laifukan da ake zarginsu dasu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel