Cika shekaru 60 a rayuwa: Buhari ya yi ma Garba Shehu kyakkyawar shaida

Cika shekaru 60 a rayuwa: Buhari ya yi ma Garba Shehu kyakkyawar shaida

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jinjina ma babban hadiminsa a kan harkokin kafafen watsa labaru, kuma mai magana da yawunsa, watau kaakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu yayin daya cika shekaru 60 a rayuwa.

A ranar Laraba, 27 ga watan Nuwamba ne Garba Shehu wanda aka haifeshi a garin Dutse a shekarar 1959 ya cika shekaru 60 a duniya, kuma shugaba Buhari ta bakin hadiminsa a kan watsa labaru, Femi Adesina ya taya shi murna, tare da masa kyakkyawar shaida.

KU KARANTA: Kaico! Jami’in Dansanda ya bindige kansa saboda an hana shi karin girma a aikinsa

Haka zalika shugaban kasa ya taya iyalai, yan uwa da abokan arzikin Garba Shehu murnar wannan rana, inda yace tun a shekarar 2015 yake aiki tare da Garba Shehu, kuma yana jin dadin hakan.

“Ina jinjina maka cimma wannan nasara, ka cancanci duk wani abu mai kyau da ka samu zuwa yanzu, ka kareni a lokutan da nake bukatar kariya yadda ya kamata, don haka ina tayaka murna. Kuma ina fatan Allah Ya tsawaita rayuwarka tare da kyakkyawar lafiya” Inji Buhari.

Bugu da kari, ma’aikatan sashin yan jaridu na fadar shugaban kasa sun taya Malam Garba Shehu murna a wani dan kwarya kwaryan taro da suka shirya masa a fadar gwamnati dake Abuja, kamar yadda kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito.

Da yake jawabi a yayin taron, shugaban sashin watsa labaru na fadar gwamnati, Malam Ubale Musa ya taya Garba Shehu murna, sa’annan ya yi adduar Allah Ya kara masa lafiya da kuma basira.

A nasa jawabin, mai gayya mai aiki, Malam Garba Shehu ya bayyana farin cikinsa game da soyayya da kauna da yan jaridun fadar shugaban kasa suka nuna masa, inda yayi dauki alwashin cigaba da aiki tare dasu cikin girmamawa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel