EFCC ta cafke 'Ibrahim Magu' na bogi kan zargin karbar rashawa

EFCC ta cafke 'Ibrahim Magu' na bogi kan zargin karbar rashawa

Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta cafke 'Ibrahim magu' na bogi a ranar Laraba a Fatakwal. Ana zarginsa da amfani da sunan shugaban hukumar wajen cin zarafi tare da barazana ga wasu manyan jami’an hukumar habaka yankin Neja Delta, NDDC.

Ya bukaci cin hanci ne daga wajensu ta yadda zai ‘kashe’ maganar bincikarsu da aka bukaci a yi.

Ibrahim Magu na bogin an gurafanar dashi ne a gaban Jastis M. L Abubakar na babban kotun tarayya da ke Fatakwal, jihar Rivers.

A takardar da mai magana da yawun hukumar, Wilson Uwaujaren ya bada, ya ce ana zargin mutumin ne da laifuka uku wadanda suka hada da sojan gona da damfara.

DUBA WANNAN: Tirkashi: An cafke wata mata dauke da ATM 23 boye a 'gabanta'

Uwuajaren ya tabbatar da cewa, “Terfa ya shiga tsaka mai wuya ne bayan da aka kamashi a otal din Juanita, Fatakwal , jihar Rivers inda yake taro da wasu daraktoci na NDDC din. Ya ce zai cire sunayensu daga jerin sunayen da EFCC zata bincika,”

Ya kara da cewa, “An zargi cewa ya nemi daraktocin ne da sunan shine shugaban hukumar yaki da rashawar. Ya tunatar dasu binciken asusun kudin NDDC da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarni. Ya bukaci hasafi daga wajensu don share sunayensu.”

“Bincike ya nuna cewa, wanda ake zargin yana zuwa ma’aikatu da bangarorin gwamnati ne don binciko bayanai a kan mutane, hakan na taimaka masa wajen damfarar mutane.” Uwuajaren ya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel