Aiki dai: Buhari ya amince da kashe biliyoyin nairori wajen gina manyan hanyoyi a Kano

Aiki dai: Buhari ya amince da kashe biliyoyin nairori wajen gina manyan hanyoyi a Kano

Majalisar zartarwar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta amince da kashe naira biliyan 19 domin ginin wasu manyan hanyoyi a jahar Kano, jahar Oyo da kuma babban birnin tarayya Abuja.

Rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta bayyana cewa ministan ayyuka, Babatunde Raji Fashola ne ya sanar da haka yayin da yake ganawa da manema labaru bayan kammala taron majalisar a ranar Laraba, 27 ga watan Nuwamba.

KU KARANTA: Kaico! Jami’in Dansanda ya bindige kansa saboda an hana shi karin girma a aikinsa

“An gabatar da takardar bukatar gina hanyar Igboho-Oloko-Agbonle a jahar Oyo, da hanyar Gulu zuwa garin Yaba a babban birnin tarayya Abuja da kuma hanyar Sharada-Madobi-Dan Baure a jahar Kano.

“Majalsar ta amince da kashe N7.29bn a kan hanyar dake jahar Oyo, N7.593bn a kan hanyar dake babban birnin tarayya Abuja da kuma N4.510bn a kan hanyar dake jahar Kano.” Inji shi.

Haka zalika Fashola ya bayyana cewa majalisar ta amince a kashe naira miliyan 523 wajen kammala aikin hanyar Efalaye-Erimo-Iwaraja daya hada jahohin Osun da Ekiti, aikin da yace an fara shi tun shekarar 2009, kuma an yi kashi 85 na aikin.

Daga karshe Fashola ya shaida ma majalisar cewa a yanzu haka suna aiki a kan hanyoyi 524 a cikin Najeriya, haka zalika suna gudanar da aikin gina tituna guda 43 a cikin manyan jami’o’In Najeriya guda 10.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci zaman majalisar zartarwa daya hada kafatanin ministocin gwamnatin Najeriya, daya gudana a ranar Laraba, 27 ga watan Nuwamba a fadar gwamnatin Najeriya, Aso Rock Villa.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, sakataren gwamnatin Najeriya, Boss Gida Mustapha, shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Najeriya, Abba Kyari da kuma shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Online view pixel