Fallasa: Yari ya tona wani sirrin Matawalle

Fallasa: Yari ya tona wani sirrin Matawalle

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya bayyana yadda tsohon gwamna, Abdulazizi yari, ya biya kansa kusan naira miliyan dari uku kafin ya bar kujerarsa a watan Mayu.

Matawalle ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, yayin da yake mika dokar soke biyan tsofaffin gwamnoni, mataimakansu da kakakin majalisar jihar kusan naira biliyan daya duk shekara.

Ya tabbatar da cewa "sabuwar dokar da aka gaggauta amincewa da ita a tsohuwar gwamnatin, bata duba halin da tattalin arzikin jihar yake ciki ba."

Matawalle ya yi alkawarin cewa, mulkinsa zai biya alawus ne kawai wanda hukumar kudin shiga ta amince.

"Na sha mamaki lokacin da na samu wasikar tsohon gwamna Yari a kan na ki biyansa kudadensa. Tsohon gwamnan ya yi barazana ga mulkina da kotu. Na kira taro da mataimakina tare da kakakin majalisar jihar kuma mun amince da cewa bamu bukatar wani alawus bayan munyi murabus." Matawalle ya ce.

DUBA WANNAN: Hanyoyi biyu da Tinubu zai iya samun takarar shugaban kasa a 2023

"Gwamnatin da ta gabata, ta bar bashin kusan naira biliyan goma na fanshon ma'aikatan kananan hukumomi, malaman makaranta da ma'aikatan gwamnatin jihar. Bayan kuma sauran basussukan da zasu iya jefa jihar cikin halin rashin kudi." ya kara da cewa.

"Tsohon gwamnan na bukatar gwamnatin jihar da ta dinga biyansa naira miliyan 120 duk wata. Hakan kuma ya zama fansho dinsa har karshen rayuwa. Ya bukaci gwamnatin jihar ta siya masa ababen hawa biyu tare da canza mishi da wasu duk bayan shekaru hudu,

"Kudin asibitinsa da iyalansa tare da hutu a gida Najeriya da ketare duk ya rataya a wuyan gwamnatin jihar, tsohon gwamnan ya bukaci gwamnatin jihar ta siya masa gida mai dakunan bacci 5 a duk jihar da ya zaba a kasar nan,

"Idan muka bar wannan dokar, zata karasa lashe albarkataun jihar a lokacin da yakamata a dinga biyansu kudi kalilan na fansho tare da sauran ma'aikatan gwamnati da suka yi murabus." in ji Matawalle.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel