Dino Melaye ya roki INEC da ta dage zaben Kogi ta Yamma, ya bada dalili

Dino Melaye ya roki INEC da ta dage zaben Kogi ta Yamma, ya bada dalili

Sanata Dino Melaye, dan takarar kujerar sanata mai wakiltar jihar Kogi ta Yamma a karkashin jam'iyyar PDP, ya roki hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC da ta dage maimaita zaben, matukar ta san ba zata iya yin zaben a duk akwatunan da yakamata ba.

Melaye ya sanar da hakan ne a yayin zantawa da manema labarai a hedkwatar hukumar INEC da ke Abuja. Ya garzaya babban ofishin hukumar ne don kara mika wani koken a kan zaben ranar Asabar 16 ga watan Nuwamba da aka yi.

Bayan mika wasikar da ya kira da "karin koke", Dino Melaye ya shafe sa'a daya tare da kwamishinan hukumar zaben mai zaman kanta ta kasa, May Agbamuche-Mbu, a tattaunawar sirri.

DUBA WANNAN: Hanyoyi biyu da Tinubu zai iya samun takarar shugaban kasa a 2023

Dino ya ce, "Abinda muka garzayo muka kawo a yau shine fam EC8B na gunduma ta daya da ke karamar hukumar Lokoja, inda INEC ta soke akwatuna 9 cikin 23 na sakamakon zabensu."

Ya kara da cewa, an soke sakamako a sauran akwatunan yayin tattara sakamakon. Wuraren da hakan ta faru sun hada da Abugi, Ole da sauran wuraren. Amma kuma ba a bayyana hakan ba yayin da INEC din ta ke sanar da wuraren da za a sake zabe a ranar 30 ga watan Nuwamba.

"Abinda muke cewa shine: ta yaya INEC zata soke wadannan akwatunan yayin tattara sakamako amma kuma bata saka su cikin inda za a kara yin zabe ba? Nasan shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ba zai san hakan ba kuma yayi shiru." Inji Dino.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel