Rashin Alkali ya tsaida shari’ar Farfesa Maurice Iwu a babban kotun Legas

Rashin Alkali ya tsaida shari’ar Farfesa Maurice Iwu a babban kotun Legas

Ranar da aka sa domin shari’ar tsohon shugaban hukumar INEC mai gudanar da zabe a Najeriya, Farfesa Maurice Iwu, ta zo ta wuce ba tare da an soma shari’ar ba saboda rashin Alkalai.

Kamar yadda mu ka samu labari a farkon makon nan, Alkali mai shari’a Nicholas Oweibo, wanda ya kamata ya saurari wannan shari’a bai zauna a kan kujerarsa a Ranar Litininin dinnan ba.

Hukumar EFCC mai yaki da Barayi ta na zargin Farfesa Maurice Iwu da laifuffuka uku a gaban kotun tarayya da ke Legas. Wadannan laifuffuka sun hada satar dukiya da almundahana.

A Ranar 8 ga Watan Agusta aka fara gurfanar da Maurice Iwu a kotu. Idan ba ku manta ba, a nan ne Alkali Chuka Obiozor ya bada belinsa a kan dunkulen kudi har Naira biliyan guda.

KU KARANTA: Ana zargin Ma'aikatan gidan yari da wawuran makudin kudi a Najeriya

A Ranar 24 ga Watan Agusta aka sake shiga kotu da Iwu bayan an maida kararsa hannun Nicholas Oweibo. A wannan ranar ne aka dage shari’ar zuwa Ranar 25 ga Watan Nuwamba.

A zaman da aka yi a baya, Farfesan ya fadawa kotu cewa bai aikata laifuffukan da ake tuhumarsa da su ba. Wannan ne dalilin dage zama zuwa makon nan domin a fara sauraron karar.

Ganin cewa Alkali bai hallara ba, aka dage wannan zama sai Ranar 27 ga Watan Fubrairun 2020. Wannan na nufin ba za a saurarin karar da EFCC ta kawo ba sai nan da watanni uku.

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa ta bakin Lauyanta, Rotimi Oyedepo, ta fadawa kotu cewa ta na zargin Maurice Iwu da lakume Biliyan 1.23.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel