Abin mamaki: Likita ya ciro kifi mai rai a hancin wani yaro

Abin mamaki: Likita ya ciro kifi mai rai a hancin wani yaro

- Wani kwararren likita mai suna Dakta Kathiravan ya yi nasarar zakulo kifi daga hancin wani yaro

- Kifin ya shige hancin Arul Kumar ne bayan da ya fada wata katuwar rijiya da ke kusa da gidansu

- An yi nasarar fito da yaron amma sai aka gano cewa ya samu matsalar numfashi, lamarin da yasa aka je asibiti

Wani kwararren likita da ke yankin kudancin kasar Indiya ya samu nasarar ciro kifi a cikin hancin wani yaro. Tun farko dai, yaron ya gamu da wannan matsalar ne tun bayan da ya fada wata katuwar rijiya da ke kusa da gidansu a jihar Tamil Nadu da ke kasar Indiya.

A lokacin da yaron ya fada ruwan da ya kusa shanye shi, kifin yayi nasarar shigewa yaron hancinshi.

A bangaren liktan kuwa, Dakta Kathiravan, ya bayyana yadda aka kawo yaron mai suna Arul Kumar, cikin halin rashin lafiya. Yaron ya samu matsala ne ta yadda yake numfashi da kyar.

KU KARANTA: Tashin hankali: Jirgi ya mutu a sararin samaniya da fasinjoji a ciki yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Abuja

A haka ne suka bazama tare da fara binciken meke damun yaron. Bayan dogon bincike ne aka gano cewa kifi ne ya shige ta kofar hancin Arul Kumar.

Likitan ya yi bayanin yadda suka shafe tsawon mintuna 30 kafin su yi nasarar zakulo kifin daga hancin yaron. Al’amarin da ya bar mutane da yawa cikin mamaki da al’ajabi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel