Tashin hankali: Jirgi ya mutu a sararin samaniya da fasinjoji a ciki yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Abuja

Tashin hankali: Jirgi ya mutu a sararin samaniya da fasinjoji a ciki yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Abuja

- Hankulan mutane da yawa da suke cikin jirgin sama mai lamba BA083 ya tashi a lokacin da suke kan hanyar zuwa Abuja

- Fasinjojin sun yi tsoron rasa rayukansu ne sakamakon inji jirgin daya da ya lalace yayin da suke sama

- Tuni dai matukan jirgin suka zabi komawa filin sauka da tashin jiragen sama da ke Heathrow a birnin Landan

Hankulan mutane da yawa ya tashi sakamakon tsoron rasa rayukansu. Jirgin kamfanin British Airways da ya taso daga Landan zai sauka a Abuja, ya rasa injinshi daya yayin da yake kan hanya a jiya Talata.

Dole ta sa jirgin saman ya juya zuwa filin tashi da saukar jiragen sama na Heathrow da ke birnin Landan.

Kamfanin jirgin saman ya tabbatar da cewa, jirgin kamfanin ya koma filin jiragen sama na Heathrow da ke Landan ne bayan al’amarin gaggawa da ya sameshi. An yi hakan ne don gujewa aukuwar wani mugun lamari.

“Jirgin saman kamfaninnan ya samu wata karamar matsala, kuma matukan jirgin sun yanke shawarar komawa filin jirgin Heathrow. A duk lokacin da wani abun gaggawa ya taso a jirgin sama wannan ce al’adar.”

“Bayan isar jirgin saman filin jirgin. Kungiyoyinmu sun kula da kwastomominmu a daren da ya gabata. An samar musu da wajen kwana. Muna masu ban hakuri ga kwastomominmu sakamakon tsaikon da suka samu a tafiyarsu.”

KU KARANTA: Dandalin Kannywood: Abin da ya sa na daina harkar fim - Jaruma Samira Saje

Idan zamu tuna, Legit.ng ta ruwaito yadda wani jirgi ya koma filin tashi da saukar jiragen sama na Murtala Muhammedd da ke Legas bayan mintuna goma da tashinshi.

Hakan ya biyo bayan hayakin da ya fara ne yayin da ya lula sararin samaniya. An gano cewa, wata fasinja ce ta zurma katon hijabi inda ta samu shigewa da shisha cikin jirgin. Bayan dagawar jirgin ne, ta fara shan shisha a bandakin jirgin.

Tuni dai aka dakatar da ita tare da sanar mata ba a shan ire-iren wadannan abubuwan a jirgin sama. Amma babu dadewa sai hayaki ya taso daga bandakin jirgin, dalilin da yasa matukan suka hanzarta komawa filin jirgin saman.

Tuni dai jami’an tsaro suka cafke budurwar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel