Tirkashi: Wani dan kato da gora ya kashe mutumin da ya kama yana lalata da matarsa

Tirkashi: Wani dan kato da gora ya kashe mutumin da ya kama yana lalata da matarsa

- Rundunar ‘yan sandan jihar Osun ta kama wani mutum mai suna Oyejide Emmar da laifin kisan kai

- Oyejide ya hallaka wani mutum mai suna Otunba ne bayan da ya zargsehi da kwartanci da matarshi

- An gano cewa, Oyejide ya daki Otunba da wani ‘zoben sihiri’ ne, lamarin da yasa ya fadi inda daga baya ya rasu

Hukumar ‘yan sandan jihar Osun ta cafke wani dan kungiyar sintiri, Emmar Oyejide, a kan zarginshi da ake da kashe wani mutum mai suna Fatai Adegboye wanda aka fi sani da Otuba.

Fatai, dan kungiyar Oodua People’s Congress, ya fadi ya mutu ne bayan da ya samu wata hatsaniya da Oyejide a sa’o’in farko na safiyar Lahadi.

An gano cewa, mazan biyun sun yi fada ne a Ipetumodu, wani gari da ke karamar hukumar Ife ta Arewa a jihar Osun.

Kamar yadda rahoto ya nuna, Oyejide, wanda asalin dan yankin Sooko ne, ya zargi mamacin da mu’amala da matarshi.

KU KARANTA: Tirkashi: Karuwa ta cakawa saurayinta wuka ya mutu har lahira bayan yayi mata cikin shege yace a zubar da shi baya so

Amma kuma, mamacin ya musanta wannan zargin. Oyejide da wasu mutane hudu duk basu yarda da maganar da mamacin ya sanar musu ba.

Bayan haka ne fada ya sarke tsakaninsu. An gano cewa Oyejide ya daki mamacin da wani zoben sihiri, wanda hakan ya sa ya fadi kasa. Daga baya kuwa aka sanar da cewa rai yayi halinshi a babban asibitin garin.

Mukaddashin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Mustapha Katayeyanjue, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin yace, kwamishinan ‘yan sandan jihar ya umarci a fara bincike don gano gamsassun dalilan da suka kawo mutuwar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel