Lalacewan jirgin kasa: Ku yi mana afuwa, komai ya dawo dai-dai - NRC ta nemi uzuri wurin fasinjoji

Lalacewan jirgin kasa: Ku yi mana afuwa, komai ya dawo dai-dai - NRC ta nemi uzuri wurin fasinjoji

Kamfanin sufurin jiragen kasan Najeriya NRC ta nemi afuwan yan Najeriya kan lalacewan jirgin Abuja zuwa Kaduna a daren Talata, 26 ga watan Nuwamba, 2019.

Mataimakin kakakin kamfanin, Yakub Mahmood, ya bayyana hakan cikin jawabin da ya aikawa kamfnain dillancin labaran Najeriya NAN a Abuja.

Yace: "Kamfanin NRC tana mai nuna nadamarta kan lalacewar jirgin karshe na Abuja zuwa Kaduna ranar Talata a kusa da tashar Rigasa."

"NRC na baiwa dukkan fasinjoji hakuri kan rashin jin dadin da suka samu sakamakon hakan."

Yakub Mahmood ya kara da cewa komai ya dawo dai-dai yanzu.

DUBA NAN Yara milyan daya da rabi basu zuwa makaranta a Kano, 946,000 a Katsina

Mun kawo muku rahoton cewa Fasinjojin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja sun shiga halin ha'ula'i yayinda jirgin ta samu matsala cikin daji kusa da tashan RIgasa wanda ya tilastasu takawa da kafa zuwa tashan karshe.

Wasu fasinjojin sun bayyana manema labarai cewa jirgin ya tashi daga Abuja misalin karfe 6 na yamma amma ta samu matsala kimanin mita 100 da Rigasa misalin karfe 8 na dare.

Daya daga cikin fasinjojin mai suna Sani Lawal, ya bayyana cewa: "Ma'aikatan sun fada mana cewa sai an dauki sa'o'i uku kafin wata jirgi ta zo daga Abuja domin karasawa damu. Sai mutane suka fara fitowa kawai suna takawa zuwa Rigasa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel