Yara milyan daya da rabi basu zuwa makaranta a Kano, 946,000 a Katsina

Yara milyan daya da rabi basu zuwa makaranta a Kano, 946,000 a Katsina

Kwamitin tallafin kula da yara ta majalisar dinkin duniya wato UNICEF ta ce akalla yara milyan daya daga rabi a jihar Kano ba su zuwa makaranta, hakazalika 946,000 a jihar Katsina.

Shugaban ofishin UNICEF dake jihar Kano, Maulid Warfa, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a jihar Katsina inda aka shirya waksho kan jihar Kano da Katsina.

Ya ce jihar Kano ta fi kowace jihar Najeriya yawan kananan yara marasa zuwa makaranta.

A cewarsa, idan aka hada yawan Malaman jihar Kano da daliban, malami daya ne ga dalibai 103, a jihar Katsina kuma malami 1 zuwa dalibai 92.

A bangaren loshin lafiya kuwa, kananan yara 423,934 basu samun isasshen abincin gina jiki a jihar Kano. A jihar Katsina kuwa, yara 312,182.

A wani labarin daban, Kwantrolan hukumar kwastam shiyar Zone B, jihar Kaduna, Mustapha Sarkin Kebbi, ya bayyana cewa hukumar ta gano hanyoyi 2000 da ake amfani da shi wajen fasa kwabrin shinkafa da wasu haramtattun kayayyaki ta Arewacin Najeriya.

Ya ce hukumar kwastam ba tada karfin ma'aikatan da zasu tsare dukkan wadannan barayin hanyoyin amma suna iyakan kokarinsu wahen tabbatar da cewa shinkafar wajen ba su shigowa Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel