Kaico! Jami’in Dansanda ya bindige kansa saboda an hana shi karin girma a aikinsa

Kaico! Jami’in Dansanda ya bindige kansa saboda an hana shi karin girma a aikinsa

Wani jami’in rundunar Yansandan Najeriya, Paul Joseph ya aikata ma kansa aika aika ta hanyar daukan ransa da kansa sakamakon kwashe tsawon lokaci ba tare da ya samu karin girma a aikinsa ba.

Jaridar Punch ta ruwaito dansandan mai mukamin Sajan ya dade yana sa ran samun karin girma zuwa Inspekta tsawon lokaci, amma karin girman ya ki yiwuwa, don haka a ranar Laraba, 27 ga watan Nuwamba ya kashe kansa bayan ya isa wajen aikinsa, inda yake gadin wani banki a jahar Imo.

KU KARANTA: Aminai na gaske: Jerin mutane 7 dake tare da shugaba Buhari tun siyasar 2003

Rahotanni sun bayyana cewa Paul, wanda dan asalin jahar Taraba ne ya dade yana korafi game da rashin samun cigaba a aikinsa, bisa dukkan alamu wannan matsala ta rashin samun karin girma ta tsaya masa a rai.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa: “A yayin da muke shiga banki domin fara aiki ne muka ji karar harbin bindiga daga bakin kofar shiga bankin, da muka tambaya, sai aka fada mana wani Dansanda ne ya kashe kansa.”

Da majiyarmu ta tuntubi kaakakin rundunar Yansandan jahar Imo, Orlando Ikeokwu, ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda tace a yanzu haka rundunar ta mika gawar mamacin zuwa dakin ajiyan gawarwaki.

A wani labarin kuma, wata kotun shari’ar Musulunci dake zamanta a unguwar Tudun Wada Zaria ta yanke ma wani matashi, Mohammed Abdullahi hukuncin zaman gidan kaso tsawon watanni 6 a kan satar wayar salula ta N10,000 a Masallaci.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito dansanda mai shigar da kara, Sajan Adamu Yahaya ya bayyana ma kotu cewa barawon ya kutsa kai cikin wani Masallaci dake filin Mallawa, Tudun Wada Zaria da sunan zai yi sallah, amma sai ya sace wayar wani mutumi da kudinta ya kai N10,000.

Dansandan ya cigaba da cewa sauran masallata ne suka ankara, inda suka bi barawon a guje, inda bayan sun kama shi sai suka mika shi ga ofishin rundunar Yansandan Najeriya dake unguwar Tudun Wada Zaria.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Online view pixel